Bayelsa: Tsohon Gwamna da PDP su na lallabar Timi Alaibe ya janye kara a kotu

Bayelsa: Tsohon Gwamna da PDP su na lallabar Timi Alaibe ya janye kara a kotu

Jam’iyyar PDP da ta karbe mulkin jihar Bayelsa a kotun koli ta fara rokon Timi Alaibe ya janye karar da ya shigar ya na kalubalantar takarar gwamna mai-ci Douye Diri.

Timi Alaibe wanda ya yi takarar tikitin jam’iyyar PDP tare da Douye Diri ya na kalubalantar yadda aka ba gwamnan jihar tutar jam’iyya a zaben da aka yi a shekarar bara.

Alaibe ya kai kara a kotu ne jim kadan bayan kammala zaben fitar da gwanin PDP, ya na zargin gwamna da jam’iyyarsa ta sabawa dokoki da ka’idojin tsaida ‘Dan takara.

PDP ta na gudun irin abin da ya faru da jam’iyyar APC a jihar ya faru da ita a kotu don haka ta ke kokarin shawo kan Timi Alaibe ya janye korafin da ya kai gaban Alkali.

Jam’iyyar APC ta gamu da cikas a kotu ne a sakamkon takardun bogin da ‘Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa ya gabatarwa hukumar zabe na kasa.

KU KARANTA: Oshiomole da Sylva su ka sa sa PDP ta karbe Bayelsa - Kpodoh

Bayelsa: Tsohon Gwamna da PDP su na lallabar Timi Alaibe ya janye kara a kotu
Timi Alaibe ya na kalubalantar tikitin da aka ba Douye Diri a kotu
Asali: UGC

PDP ta na jin tsoron cewa Timi Alaibe ya na da hujjoji masu karfi a gaban babban kotun tarayya wanda za su iya jawo mata matsala duk da an rantsar da Sanata Douye Diri.

Bisa dukkan alamu nan ba da dadewa ba za a saurari karar Alaibe da PDP a kotu. Da farko PDP ba ta damu da karar ba, ganin cewa APC ta tika ta da kasa a zaben gwamnan.

Tsohon gwamna Seriake Dickson ya na daga cikin masu kokarin rokon Cif Timi Alaibe ya hakura da shari’ar da ya ke nema ayi da ‘Yanuwansa na jam’iyyar PDP mai mulki.

Ana rade-radin cewa Alaibe ya na da goyon bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu Jiga-jigan PDP, wanda wasunsu su ka yi wuf su ka koma jam’iyyar APC.

Bayan kokarin da Seriake Dickson ya fara yi na dinke sabanin da ke cikin PDP, sabon gwamna Douye Diri ya gana da Goodluck Jonathan a gidansa bayan ya shiga ofis jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel