Dahiru Bauchi da 'ya'yansa uku sun ziyarci Buhari a Villa (Hotuna, bidiyo)
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin babban malamin addinin Islama kuma jigo a tafiyar darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a fadarsa, Villa, da ke Abuja a ranar Lahadi.
Babban malamin ya samu rakiyar 'ya'yansa guda uku, a cikinsu akwai Sheikh Ibrahim Dahiru Usman.
A cikin takaitaccen faifan bidiyo da hotunan da hadimin shugaban Buhari mai suna Buhari ya Sallau ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Sheikh Bauchi ya yi wa shugaba Buhari da kasa addu'o'in samun zama lafiya da karin yalwar arziki.
A daya daga cikin hotunan da Sheikh Bauchi suka yi tare da Buhari, an ga ministan ilimi na kasa, Adamu Adamu, tare da wasu hadiman shugaban kasa.
A wani labarin mai nasaba da Sheikh Bauchi, jikarsa, Rukayyatu Fatahu Umar ta zamo daya cikin yara Musulmai kanana a duniya da suka haddace Al-Qur'ani mai girma.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne ya haifi Sayyada Maimunatu, wacce rahotanni suka bayyana cewa ita ce ta haifi Rukayyatu.
DUBA WANNAN: Buhari ya aminta da bawa masana'antun waka da fim tallafin N7bn
Karamar yarinyar ta fara haddar Qur'ani ne a wata makarantar Islamiyya da kakanta ya kafa. Makarantar kuwa na karkashin kular mahaifiyar yarinyar ne Sayyada Maimunatu.
Makarantar na nan ne a Bakin Ruwa a Kaduna.
Kamar yadda mahaifiyar yarinyar ta sanar, diyarta ta haddace littafin mai girma ne a lokacin da ta cika shekaru uku da watanni takwas a duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng