Wike: Oshiomhole ya sauka daga kujerar APC na gaza hana rantsar da Diri

Wike: Oshiomhole ya sauka daga kujerar APC na gaza hana rantsar da Diri

A jiya Ranar Asabar, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Adams Oshiomhole, ya sauka daga kujerar da ya ke kai.

Mai girma Nyesom Wike ya bukaci Adams Oshiomhole ya bar mukaminsa na shugaban APC na kasa ne bayan ya gaza hana a rantsar da Duoye Diri matsayin gwamna.

Mista Wike ya yi wannan kira ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai a Garin Fatakwal, a Ranar 15 ga Watan Fubrairun 2020 kamar yadda mu ka samu labari.

A cewar gwamnan, Adams Oshiomhole, ya yi yunkurin karbe jihar Ribas daga hannun PDP. Wike ya ke cewa mutanen jihar Ribas ba su bari an yi masu fashin kuri’u ba.

Nyesom Wike ya caccaki shugaban APC ya na cewa: “Najeriya kasa ce da za ka ga mutane marasa daraja. Abin da za ka ji sun fada yau dabam da abin da za su fada gobe.”

"Ina tunanin Adams Oshiomhole a matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC, ba mutum mai daraja ba ne, kuma bai kamata wani ya yi wata harka da shi ba.” Inji Wike.

KU KARANTA: Douye Diri ya ziyarci tsohon Shugaban kasa Jonathan a Bayelsa

Wike: Oshiomhole ya sauka daga kujerar APC na gaza hana rantsar da Diri
Wike ya ce Oshiomhole ba zai iya takawa hukuncin kotun koli burki ba
Asali: Depositphotos

“Na farko, ban taba tada rigima ba, kuma ba zan taba yi ba. Amma idan ka ga ‘Yan fashi a cikin gidanka, ba za ka tsaya ka na lallabarsu cewa su yi hakuri su fita ba.”

“Mutane su na tunanin cewa ‘Yan fashi su ne wadanda su ke dauke kudin jama’a. Mafi munin fashi shi ne fashin kuri’u kamar yadda kowa ya san Oshiomhole.”

“Ya dauka cewa tun da ya na jam’iyya mai mulki, zai iya amfani da karfin Soji, ya sace kuri’un jama’a. An koya masa hankali, ya koyi mummunan darasi.” Inji Wike.

Wike ya kara da cewa: “Idan ka zo murde mana zabe, jama’a za su yi abin da ya dace. Oshiomhole ya dauka babu wanda zai iya masa komai don su na rike da mulki”

Gwamnan ya shiga tarihi, ya bada labarin yadda ya samu matsala da Oshiomhole a lokacin Goodluck Jonathan, ya ce babu yadda zai yi da hukuncin kotun koli.

“Meyasa su ka gaza iya fitar da ‘Yan takara a Ribas da Zamfara? Oshiomhole ne ya jawowa APC wannan matsala a Bayelsa. Ka da a rika daukar shi wani Mutum.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng