Oshiomhole da Sylva su ka ja Jam’iyya ta rasa Jihar Bayelsa a Kotu – Kpodoh

Oshiomhole da Sylva su ka ja Jam’iyya ta rasa Jihar Bayelsa a Kotu – Kpodoh

Perekeme Kpodoh, wanda ya na cikin manyan Jagororin jam’iyyar APC a Bayelsa ya bayyana abin da ya sa su ka rasa kujerar gwamna sakamakon hukuncin Alkalan kotun koli.

Mista Perekeme Kpodoh ya bayyana cewa Adams Oshiomhole wanda ke rike APC a Najeriya, da karamin Ministan harkar man fetur, Timipre Sylva, su na da hannu a rasa kujerar jihar.

Kpodoh ya ke cewa ya kamata jam’iyya ta kama Adams Oshiomhole da kuma Timipre Sylva da laifin jawo mata rasa kujerar gwamna daidai lokacin da ake shirin shiga gidan gwamnati.

‘Dan siyasar ya bayyana cewa wannan hukunci na kotun koli ya kunyata gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC a sakamakon aikin wadannan jiga-jigan jam’iyyar.

A cewar Kpodoh, tsohon gwamna Sylva ya jawo rikici a tafiyar APC a jihar Bayelsa ta hanyar watsi da wadanda su ka yi wa jam’iyya bauta. “Su ka je su kawo mutum maras satifiket.”

Oshiomhole da Sylva su ka ja Jam’iyya ta rasa Jihar Bayelsa a Kotu – Kpodoh
Kpodoh ya ce Oshiomhole da Sylva su ka hana Lyon zama Gwamna
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayelsa: Douye Diri ya ce zai jawo 'Yan APC da PDP a Gwamnatinsa

“Ka kawo mutum mai takardun shaidar karatun bogi, sannan ka ce kai ne shugaban jam’iyya. Kafin kotun koli ta yi hukunci, har Sylva ya zabi wadanda gwamna Lyon zai ba mukami.”

"Da ace Lokpobiri ne, da abubuwan nan ba su kare haka ba. Mun fadi wannan a baya, amma babu wanda ya saurare mu.” Kpodoh ya ce yanzu a karshe APC ta yi asarar dukiya a banza.

‘Dan siyasar ya ke cewa kawo Tiwe Orunimigha da aka yi a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar Bayelsa, shi ne abin da ya faro jawo matsala tsakanin Sylva da sauran 'yan jam’iyya.

“Alhaki ke nan. Idan ka yaudari jama’a, Ubangiji zai yi maka hukunci. Ya kamata Oshiomhole ya rika sauraron maganganun ‘Ya ‘yan jam’iyya daga yanzu.” Inji Perekemeh Kpodoh.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel