Douye Diri ya ziyarci Goodluck Jonathan a gidansa, ya na neman hadin-kai

Douye Diri ya ziyarci Goodluck Jonathan a gidansa, ya na neman hadin-kai

Sabon gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya fara daukar matakai domin ganin an dinke barakar da ke cikin jam’iyyarsa ta PDP wanda ta samu mulki a hannun kotun koli.

A Ranar Asabar Sanata Douye Diri ya kai wa tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ziyara saboda sasanta rigimar cikin gidan da PDP ta ke fama da shi a Bayelsa.

Mai girma Douye Diri ya yi magana da ‘Yan jarida bayan zaman na su, inda ya shaida cewa wannan ne matakin farko da ya dauka na dinke barakar da ke jam'iyyar PDP.

Sabon gwamnan ya yi wannan ne domin kawo zaman lafiya da hadin-kan ‘Ya ‘yan PDP a Bayelsa da fadin kasa baki daya. Gwamnan ya ce zai dama da ‘Yan APC da PDP.

Diri ya ce: “Mu na bukatar abin da zai jawo kowa, ya hada kan jama’a. An zabe mu gwamna ne ba na PDP ba kawai, na dukannin jihar Bayelsa. Kowa zai ji ana yi da shi.”

KU KARANTA: Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya tsallake rijiya da baya

Douye Diri ya ziyarci Goodluck Jonathan a gidansa, ya na neman hadin-kai
Gwamna Diri ya gana da Jonathan daga hawa kujerar mulki
Asali: Twitter

Goodluck Jonathan ya rike kujerar mataimakin gwamna sannan kuma ya yi gwamna a jihar Bayelsa. Har gobe ya na cikin masu fada a ji a Najeriya da kuma jihar ta sa.

A Asabar din, Diri ya gabatar da shaidar da hukumar zabe na INEC ta mika masa a gaban tsohon shugaban kasar. An rantsar da gwamnan ne a Ranar 14 ga Watan Fubrairu.

Ana zargin cewa Goodluck Jonathan da Mabiyansa sun marawa Timi Alaibe baya ne a zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP, amma a karshe Douye Diri ne ya samu tikiti.

Yanayin yadda aka gudanar da zaben fitar da gwanin ya jawowa gwamna (na lokacin) Seriake Dickson da Douye Diri cikas har ta kai wasu su ka sauya-sheka zuwa APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel