Namibia: Matar shugaban kasa za ta bayar da dukiyarta sadaka

Namibia: Matar shugaban kasa za ta bayar da dukiyarta sadaka

- Matar shugaban kasar Namibia ta dauki alkawarin sadaukar da dukiyarta bayan mutuwarta

- An yi hasashen cewa Monica Geingos na da dukiyar da ta kai dala miliyan uku, wanda aka ce ta shirya sadaukarwa ga gidauniyarta

- Gidauniyar tata kan ba da tallafi ga masu kananan masana’antu da kuma dalibai marasa galihu da aka ci mutuncinsu

Rahotanni sun kawo cewa uwargidar shugaban kasar Namibia ta dauki alkawarin sadaukar da dukiyarta bayan mutuwarta.

An yi hasashen cewa Monica Geingos na da dukiyar da ta kai dala miliyan uku, wanda aka ce ta shirya sadaukarwa ga daya daga cikin gidauniyoyinta domin taimakawa jama’a.

Namibia: Matar shugaban kasa za ta bayar da dukiyarta sadaka
Uwargidar shugaban kasar Namibia, Monica Geingos tare da takwararta ta Najeriya, Aisha Buhari
Asali: Twitter

Gidauniyar tata kan ba da tallafi ga masu kananan masana’antu da kuma dalibai marasa galihu da aka ci mutuncinsu.

Uwargidar shugaban kasar ta kasance lauya kuma mai kare hakkin wadanda aka zalunta.

Har ila yau ta karyata zargin cewa tana neman kujerar gwamnati.

Ms Geingos ta ce "Na yi amanna cewa gado na daya daga cikin babban abin da ke janyo rashin daidaito a tsakanin al'umma, shi yasa na yanke shawarar sadaukar da dukiyata ga mabukata".

Bayan shugaban Namibia Hage Geingob ya dare karagar mulki ne a 2015, kuma shi da matarsa Monica Geingos sun gabatar da dukiyarsu a lokacin da ta kai kusan dala miliyan takwas.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ba za a taba rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa ba - Oshiomhole

Idan za ku tuna a chan baya fitaccen attajirin nan na duniya da kuma yayi fice wajen taimakon bayin Allah mai suna Bill Gates ya shawarci daukacin attajirai da masu hannu da shunin Najeriya da su rika taimakawa marasa karfi a cikin al'ummar su.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu, yana kun she ne a cikin jawabin da shi Bill Gate din yayi yayin da yake tattaunawa da gidan jaridar Daily Trust inda yayi karin haske game da ayyukan taimakon da yake yi.

Legit.ng ta samu cewa Bill Gates din da ke zaman shugaban kamfanin kera kwamfutocin nan na Microsoft ya kuma jinjinawa attajirin nan dan asalin Najeriya daga jihar Kano watau Aliko Dangote bisa irin yadda ya dukufa wajen saukaka rayuwar masara karfi a Nahiyar ta Afrika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel