MWL: Kungiya za ta gina Makarantar N1.2b a Jihar Kaduna - Al-Hawairini

MWL: Kungiya za ta gina Makarantar N1.2b a Jihar Kaduna - Al-Hawairini

Kungiyar Muslim World League (MWL) ta Kasar Saud Arabia ta taimakawa Najeriya da makudan kudi a matsayin gudumuwar ilmin Marayu da ake da su a kasar.

Wannan kungiya ta Musulunci ta bada Naira biliyan 2.6 da nufin daukar nauyin karatun wasu Marayu 7, 600, tare da yunkurin fitar da su daga cikin kangin talauci.

MWL ita ce uwar kungiyar nan ta Islamic Organisation for Relief and Development da ke Garin Kaduna, wanda ta dauki shekaru ta na taimakawa Marayu a fadin jihar.

A cikin shekaru goman da su ka wuce, wannan kungiya ta Islamic Organisation for Relief and Development ta yi dawainiyar bukatun Marayu 10, 000 a cikin Kaduna.

Darektan wannan kungiya watau Sheikh Abdallah Bin Salim Al-Hawairini, ya tabbatar da karbar wannan makudin kudi, tare da bayyana yadda aka shirya batar da su.

KU KARANTA: An yi ram da wasu mata masu zaman kansu a jihar Jigawa

Abdallah Bin Salim Al-Hawairini ya ce za su kashe Naira biliyan 1.2 wajen gina katafariyar makarantar kananan yara a Unguwar Dosa da ke cikin Birnin Kaduna.

Shugaban wannan taro Yunus Ustaz Usman SAN, ya ba masu kula da wannan kungiya shawarar su yi amfani da kudin yadda ya dace, ba su je su karo matan aure ba.

Yunus Ustaz Usman ya bayyana cewa son kan wasu ne ya jawo sha’anin Almajiranci ya tabarbare a kasar, musamman a Yankin Arewacin Najeriya inda abin ya yi kamari.

A cewar Ustaz Usman, manyan mutane ba su bada kyauta daga cikin dukiyarsu, inda ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su zama ‘Yanuwan junansu kamar yadda addini ya ce.

“Idan har aka rike wannan tarbiya a Arewacin Najeriya, to babu shakka kasar nan baki daya za ta fita daga cikin radadin talaucin da ta ke ciki.” Inji babban Lauya Usman.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng