Sojojin Najeriya sun kama buhun shinkafa cike da alburusai a jahar Zamfara
Dakarun rundunar Sojan Najeriya dake jibge a garin Moriki na jahar Zamfara sun kama wani dan achaba dauke da buhun shinkafa wanda bincike ya fallasa ashe tarin alburusai ne makare a cikin buhun.
Jaridar Premium Times ta ruwaito majiyoyi daga rundunar Sojin Najeriya sun bayyana cewa dan Achaban ya tsere, amma an kama buhun dake dauke da alburusai 4653 samfurin 7.62mm.
KU KARANTA: Buhari ya fi kowa fahimtar matsalar tsaron da Najeriya ke fama da shi – Buratai

Asali: Facebook
Rahotanni sun bayyana cewa Sojojin sun kama alburusan ne bayan samun bayanan sirri dake nuna cewa ana safarar makamai zuwa Moriki, da wannan dalili suka sanya shingayen binciken ababen hawa a cikin garin.
“Mun sanya shigayen binciken ababen hawa kenan sai ga wani babur ya iso dauke da wani buhu kamar na shinkafa, amma direban babur din bai tsaya a bincike shi ba, sai muka bi shi da gudu, da ya ga zamu kure masa gudu sai ya jefar da babur din ya tsere.” Inji wani majiya daga rundunar Sojan.
Da wannan ne aka yi kira ga dakarun Soji dake yankin da suka kasance cikin shirin ko ta kwana domin yan bindiga da sauran miyagu suna cigaba da amfani sabbin dabaru daban daban domin safarar makamai da alburusai.
A wani labarin kuma, babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen daukan matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take.
A kwanakin baya ne majalisar dokokin Najeriya ta nemi Buhari ya sallamki kafatanin hafsoshin tsaron Najeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin gazawarsu wajen kare rayukan yan Najeriya, duba da sake farfadowar da Boko Haram ta yi.
Da wannan ne babban hafsan Sojan, Laftanar Janar Tukuru Tusuf Buratai yace: “Ba tare da kalubalantar ikon majalisa ba, amma sallamar hafsoshin tsaro ba shi bane hanyar da zai warware matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da ita.”
Buratai ya kara da cewa Buhari na sane da halin da ake ciki, kuma shi ne mai dakin, shi ya san inda ke masa yoyo, haka zalika shi kadai ne zai iya yanke hukuncin da ya kamata game da lamarin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng