Rashin gaskiya ya yi wa jama’a katutu tun kafin in hau mulki – Buhari

Rashin gaskiya ya yi wa jama’a katutu tun kafin in hau mulki – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa rashin gaskiya ya ratsa jinin ‘Yan Najeriya, don haka ake samun matsala wajen yakin da ya dauko.

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban kasar ya na kukan tun kafin hawansa mulki a shekarar 2015, rashin gaskiya da yin ba daidai ba, ya bi cikin jikin mutane.

Muhammadu Buhari ya nuna cewa sabo da rashin gaskiya ne ya sa ba a ganin tasirin kokarin da ya ke yi a wasu wurare, duk da haka ya ce ba zai ja da baya ba.

A wajen kaddamar da wani littafi da tsohuwar shugabar EFCC, Farida Waziri ta rubuta, Buhari ya ce dole a tsaya tsayin daka wajen ganin an yaki rashin gaskiya.

Shugaban Najeriyar ya yi jawabi ne wajen kaddamar da wannan littafi mai suna “One Step Ahead: Life of a Spy, Detective and Anti-Graft Czar” a Birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Abin da ya sa na tsige Waziri daga EFCC lokacin ina mulki - Jonathan

Rashin gaskiya ya yi wa jama’a katutu tun kafin in hau mulki – Buhari
Buhari ya yi magana wajen kaddamar da littafin Farida Waziri
Asali: Depositphotos

Ministan harkokin cikin-gida, Rauf Aregbesola, shi ne ya wakilci shugaban kasar wanda ya yi tafiya, ya kuma yi magana a madadinsa a wajen wannan bikin.

“Dole mu gane cewa rashin gaskiya babban kalubale ne ga gudanar da mulki da cigaba, wanda dole mu fatattakesa daga cikin tsarinmu.” Inji Shugaban kasar.

“Mun samu gagarumar nasara wajen karbo kudin da aka sace, tare da toshe kafar sata da kuma kama wadanda ake zargi da laifi, har da gurfanar da su a kotu.”

Ya ce: “Idan wasu ba su ganin tasirin aikin da mu ke yi a zahiri, saboda yadda rashin gaskiya ya shiga cikin jikinmu ne, har abin ya ratsa wurare kafin zuwamu.”

A karshen jawabinsa ta bakin Ministan, shugaban kasar ya jinjinawa Farida Waziri na rubuta labarinta a kan bakin aikin ‘Yan Sanda da kuma hukumar EFCC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel