Rashin tarbiyya da kin girmama na gaba na daga cikin manyan matsalolin Kannywood – Tsohon Furodusa

Rashin tarbiyya da kin girmama na gaba na daga cikin manyan matsalolin Kannywood – Tsohon Furodusa

Wani dattijo a harkar shirya fina-finan Hausa kuma tsohon furodusa, Malam Adamu Muhammad wanda aka fi sani da Kwabon Masoyi ya ce rashin tarbiyya da kin girmama na gaba na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar masana'antar finafinan Hausa ta Kannywood.

Tsohon furodusan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da majiyarmu ta mujallar Fim kan halin da masana'antar ta tsinci kan ta a yau.

A cewar sa, "Ita harkar fim a matsayin ta na masana'anta, ta samar da ɗimbin ayyukan yi ga matasa wanda kuma hakan wani cigaba ne da aka samu, amma babbar matsalar harkar a yanzu ita ce ƙarancin tarbiyyar yaran.

"Sau da yawa za ka je waje sai ka ga ba a ma damu da zuwan ka ba, ba a san kai wani ne ba.

"Amma dai duk da haka, ni a matsayi na na Adamu Muhammad zan iya cewa ba ni da matsala da kowa sai dai wadda ta shafi harkar baki daya."

Rashin tarbiyya da kin girmama na gaba na daga cikin manyan matsalolin Kannywood – Tsohon Furodusa
Rashin tarbiyya da kin girmama na gaba na daga cikin manyan matsalolin Kannywood – Tsohon Furodusa
Asali: Twitter

Da aka tambaye shi kan yadda za a tunkari matsalar, tsohon babban furodusan ya ce, "Kiran da zan yi shi ne su sa hankali a cikin aikin su, su cire ƙyashi da hassada, su rinƙa taimakon junan su, domin hassada da ƙyashi ne ya ke kawo fadace-fadace da tozarta juna, ta yadda har aka samu kai a halin da ake ciki a yanzu."

Malam Adamu ya kara da cewa, "Harkar fim sana'a ce, don haka su daina daukar ta da wasa, kamar yadda su ke yi mata a yanzu, domin su na ɗaukar ta a matsayin wasa ko wani dandalin nishadi.

"Saboda haka a dunga kiyayewa da kuma girmama juna, domin duk harkar da za ka ci ka sha ka yi wa kan ka sutura, to bai kamata ka ɗauke ta da wasa ba.

"Don haka a dunga kiyaye mutuncin ita kan ta sana'ar domin guje wa abin da mutane za su rinƙa ganin an yi abin da bai dace ba."

KU KARANTA KUMA: Sanata Ndume ya roki Buhari da ya kawo karshen rikicin Boko Haram

Shi dai Adamu Muhammad, tare da shi aka yanke wa masana'antar finafinan Hausa cibiya, domin kuwa ya na daga cikin furodusoshin farko.

Fim din sa mai suna 'Kwabon Masoyi', wanda ake yi masa lakabi da shi, ya na daga cikin finafinan da aka soma shiryawa aka fitar zuwa kasuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng