Nigeria Air: Gwamnati ta na nan da shirinta – Minista Inji Hadi Sirika

Nigeria Air: Gwamnati ta na nan da shirinta – Minista Inji Hadi Sirika

Ministan harkokin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa ba ayi watsi da maganar kafa kamfanin jirgin saman gwamnatin kasar na Nigeria Air ba.

Hadi Sirika ya bayyana wannan ne a Ranar Talata, 11 ga Watan Fubrairun 2020 a wajen wani taro da Ma’aikatan jiragen sama na kasar su ka shirya a makon nan.

Mai girma Ministan ya yi jawabi ne a laccar bana da aka shirya mai taken ‘Gudumuwar kamfanin jirgin saman gwamnati ga cigaban rayuwa da tattalin Najeriya.’

Darektan bincike da tsare-tsare da kuma alkaluma na Ma’aikatar, Shehu Rabiu, shi ne ya wakilci Ministan a wajen wannan biki wanda shi ne na bakwai a tarihi.

“Akwai wasu abubuwan cikin gida da mu ke kokarin shawo kansu, amma ina tabbatar maku da cewa za a kammala wannan aiki kowane lokaci daga yanzu.”

KU KARANTA: Abin da ya sa jami'ai su ka tsare jirgin Atiku - Hadi Sirika

Nigeria Air: Gwamnati ta na nan da shirinta – Minista Inji Hadi Sirika
Ministan Najeriya ya ce kamfanin Nigeria Air zai fara aiki nan gaba kadan
Asali: Facebook

Ministan ya kuma kara da ba ma’aikatan kwarin gwiwa da cewa: “Da ku za a kaddamar da shirin.” Ma’ana idan an kafa kamfanin, za a a fara aiki da su.

“Kamfanin jirgin saman Najeriya zai taimakawa tattalin arzikin kasar, kuma buri ne na kowane ‘Dan Najeriya saboda ribar da za a samu daga kamfanin.”

“Harka ce da ta ke kawo kudi, kuma mu na fatan cewa idan kamfanin jirgin ya fara aiki, Najeriya za ta shiga sahun sauran kamfanonin Duniya.” Inji Ministan

A wajen wannan taro da aka yi, shugaban hukumar FAAN mai kula da filin tashi da saukar jiragen Najeriya, Rabiu Yadudu, ya tofa albarkacin bakinsa.

Kyaftin Rabiu Yadudu ya bayyana cewa kasashen Duniya su na kafa kamfanin jirgin samansu ne domin samawa jama’a aikin yi da kuma daga martabar kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel