Covid-19: WHO ta sauya wa cutar coronavirus suna
- Cibiyar lafiya ta duniya (WHO), ta sauya wa mummunan cutar nan da ta fito daga birnin Wuhan a kasar China a ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairu suna
- Shugaban kungiyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce daga yanzu za a dunga kiran cutar da Covid-19
- Chanjin sunan na zuwa ne bayan samun karuwar mutuwar wadanda suka kamu da cutar wanda ya haura 1000
Cibiyar lafiya ta duniya (WHO), ta sauya wa mummunan cutar nan da ta fito daga birnin Wuhan a kasar China a ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairu suna.
A cewar shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a birnin Geneva ya ce daga yanzu za a dunga kiran cutar da Covid-19.
Chanjin sunan na zuwa ne bayan samun karuwar mutuwar wadanda suka kamu da cutar wanda ya haura 1000, yayin da wasu dubban mutane kuma suka kamu da ita.
KU KARANTA KUMA: Sanata Elisha Abbo ya siyi timatirin N100 kan N50k a hannun yar shekara 4 da ke talla a Adamawa
Masu bincike sun bukaci a samar da wani suna ga cutar a hukumance domin a magance rudani da kyamar da ake yi wa masu cutar.
Shugaban hukumar WHO ya ce, " Dole muka samo sunan da ba shi da alaka da sunan wani waje ko wata dabba ko wani mutum ko kuma wata kungiya ta mutane, kuma suna ne da bashi da wuyar fada ba shi kuma da alaka da sunan wata cuta".
Ya ce "Samun sunan na da matukar muhimmanci domin a kare amfani da sunan da zai iya janyo wata matsala".
An samar da sabon sunan cutar ne daga farkon sunan cutar wato haruffan "Co" daga "corona", sai "vi" daga"virus" da kuma "d" daga "disease", sannan kuma daga karshe aka sanya shekarar da cutar ta fara bulla wato 2019.
A baya mun ji cewa Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Abuja, Kano, Legas, Cross River, Akwa Ibom, Port Harcourt, Enugu, Delta da Bayelsa matsayin jihohin da ya kamata a shirya matakan tsaro idan cutar Coronavirus ta bulla a Najeriya.
Babbar jami'ar WHO, Dhamari Naidoo, ta bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata a taron horar da yan jarida kan cutar Coronavirus.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng