Yanzu-yanzu: Sojoji sun kama mayakin Boko Haram a Filato

Yanzu-yanzu: Sojoji sun kama mayakin Boko Haram a Filato

- Rundunar sojin Najeriya sun cafke wani mutum da ake zargi dan Boko Haram ne a jihar Filato

- An kama wanda ake zargin ne bayan da rundunar ta kai samame don cafke wasu bata-gari a jihar

- Wanda ake zargin ya amsa cewa shi dan kungiyar ne kuma ya gudo ne daga kauyen Damagun dake jihar Yobe

Rundunar sojin Najeriya ta musamman mai suna Operation Safe Haven sun kama wani wanda ake zargin dan Boko Haram ne. Rundunar ne masu kula da zaman lafiya a wasu sassa na jihar Filato, Bauchi da kuma jihar Kaduna.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Augustine Agundu, ya bayyana cewa wanda ake zargin mai suna Umar Musa Tello an kama shi ne a wajen caca da ke kauyen Zawurna a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, kamar yadda jaridar Daily Trust at tabbatar.

Yanzu-yanzu: Sojoji sun kama mayakan Boko Haram a Filato
Yanzu-yanzu: Sojoji sun kama mayakan Boko Haram a Filato
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce

Janar Agundu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da suka kai samame don kama wasu 'yan ta'adda da suka yi laifuka daban-daban a jihar.

Kamar yadda kwamandan ya ce, binciken farko ya bayyana cewa wanda ake zargin ya gudo ne daga kauyen Damagun da ke jihar Yobe saboda yadda Operation Lafiya Dole ke farautarsu.

Janar Agundu ya kara da cewa, wanda ake zargin ya amsa cewa shi mayakin kungiyar Boko Haram ne tun kusan shekaru uku da suka gabata amma ya yanke hukuncin tuba. Ya kara da cewa tuni ya fice daga kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel