Kebbi: Jami’an EFCC su na zargin Hukuma da cin ragowar kudin Mahajjata

Kebbi: Jami’an EFCC su na zargin Hukuma da cin ragowar kudin Mahajjata

Mun samu labari cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa sun aukawa hukumar kula da jin dadi da walwalan Alhazai na jihar Kebbi.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa EFCC ta na zargin hukumar Alhazan jihar da kin dawowa da wasu rarar kudin da aka samu daga aikin hajjin daka ayi a shekarar 2017/2018.

Kudin da ake zargin hukumar Alhazan da lamushewa zai kai Naira miliyan 90. A samamen da EFCC ta kai a ofishin, ta iya gano wasu daga cikin wannan kudi inji wani Jami’i.

Shugaban hukumar EFCC na Yankin Sokoto, Kebbi da Zamfara, Mista Abdullahi Lawal, ya shaidawa ‘Yan jarida wannan a jiya Ranar Litinin, 10 ga Watan Fubrairun 2020.

Abdullahi Lawal ya kuma tabbatarwa Manema labarai cewa EFCC ta gayyaci shugaban kwamitin maida kudin aikin hajji da Darektan harkar kudi domin yi masu tambayoyi.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Aliyu bai saci kudin Gwamnati ba inji Kotu

Kebbi: Jami’an EFCC su na zargin Hukuma da cin ragowar kudin Mahajjata
EFCC ta kama mutum uku a hukumar Alhazan Kebbi ta yi masu tambayoyi.
Asali: Facebook

Haka zalika Hukumar ta EFCC ta kira Mai kula da asusun kudin hukumar Alhazan ya yi bayani game da yadda aka batar da ragowar kudin Maniyattan Kebbi na shekarar.

“Hukumar Alhazai na kasa ta dawowa Mahajjata da kudinsu ta hannun hukumomin jihohi, kuma aka sanar da mu. Akwai bukatar ace an maidawa kowa ragowar kudinsa.”

“Ya kamata ace hukumar ta maidawa wadanda su ka sauke farali a shekarar 2017/2018 a Saudi Arabia kudinsu, amma babu shaidar da ke nuna cewa an maida kudin.”

“Wannan ya sa mu ka shigo da karfinmu domin ganin inda aka samu matsala, ko meyasa har yanzu Mahajjatan jihar ba su samu kudinsu bar har yau.” Inji Mista Lawal.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel