Nasarar kowanne mai arziki na duniya na da alaka da wanda ya zaba a matsayin abokin rayuwa - Bincike
- Nasarar ma’aurata na dogara ne da yanayin goyon baya da tallafin da suke samu daga junansu
- Manyan mutane a duniya sun tabbatar da cewa nasararsu ta dogara ne ga abokan rayuwarsu wadanda suka goya musu baya
- A binciken da aka gudanar, an gane cewa ba karin magana kadai ba ce, akwai bayani mai matukar amfani game da goyon bayan juna ga ma’aurata
Mutane da yawa kan danganta nasararsu ga wanda suka aura ko kuma suke tare da su a rayuwarsu. Sau da yawa maza na cewa, “A duk lokacin da ka ga namiji ya samu wata nasara ko ci gaba, idan ka duba za ka ga akwai mace a tare da shi”. Ma’abota bincike sun ce wannan maganar haka take ba karin magana ne kawai ba.
Binciken da aka wallafa a jami’ar Carnegie Mellon ya nuna cewa idan kana da abokin rauwa mai goyon bayanka, akwai yuwuwar samun nasara a duk abinda ka saka gaba a rayuwa. Binciken wanda aka yi shi a kan ma’aurata 163, an yi shi ne ta hanyar yin abubuwa masu tarin yawa don a gano bakin zaren.
Masu binciken sun gano cewa ma’auratan da suke goyon bayan juna sun lashe gasar da aka saka musu. Amma kuma marasa goyon bayan juna tare da kuma rige-rige da ganin kyashin juna sun fadi gasar.
Wani farfesa a fannin sanin halayyar dan Adam a kwalejin Dietrich mai suna Brooke Feeney, ya ce “Da yawa daga cikin ma’auratan da suka samu nasara a rayuwa suna danganta ta ne da abokan zamansu ta yadda suka taimaka musu. Barrack Obama ya bayyana cewa Michelle Obama ce madogararsa da yadda take goyon bayan shi a wani taro a 2011.”
KU KARANTA: Abubuwa 6 da Allah ya yiwa Musulmai ni'ima da su da ya sanya jikinsu baya wari
Obama ya ce “A bayyane yake bazan iya yin komai ba idan babu Michelle.”
Mamallakin kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Mark Zuckerberg ya bayyana yadda matar shi ke taka rawar gani a rayuwarshi. Ya sanar da hakan ne a wani jawabi da yayi a 2017 a jami’ar Harvard.
A 2013 kuwa, Beyonce ta yabawa mijinta Jay-Z ta yadda yake taimakonta da goyon bayanta a wurare da dama.
Wannan binciken kuwa ya tabbatar da gaskiyar zancen na cewa in har abokin rayuwarka na hassada ko bakin ciki da wani ci gaba game da kai, toh ba shakka babu inda mutum zai je.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng