Shugabanni na tsaron fada ma Buhari gaskiya kan ta’addanci – Shehu Sani

Shugabanni na tsaron fada ma Buhari gaskiya kan ta’addanci – Shehu Sani

- Shehu Sani ya zargi shugabanni da kin fada ma shugaba Buhari gaskiya

- Tsohon dan majalisar ya ce maimakon haka sai wadannan mutane su dunga yiwa Shugaban kasr fadanci suna yaba masa

- Sani a martani ne ga kisan da ake wa mutane a jahar Borno

- Ya ce sai dai ka ji suna 'Ranka ya dade muna godiya da kokarin da kake yi,wallahi komai dai dai ne,ba matsala'

Tsohon daan majalisar Kaduna Shehu Sani ya zargi shugabanni da kin fada ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari gaskiya.

Sani na martani ne ga kisan yan Najeriya 30 da yan ta’addan Boko Haram suka yi Maiduguri, jahar Borno.

Shugabanni na tsaron fada ma Buhari gaskiya kan ta’addanci – Shehu Sani
Shugabanni na tsaron fada ma Buhari gaskiya kan ta’addanci – Shehu Sani
Asali: UGC

Sanatan ya ce wadanda ke samun damar ganin Shugaban kasar sun gwammaci su yi ta yi masa fadanci da kirari maimakon su fadi gaskiya game da halin da aubuwa ke ciki a kasar.

KU KARANTA KUMA: Korarrun ma’aikatan jahar Adamawa 10,000 sun gudanar da zanga zanga a Yola

“Kada mu ga laifin Shugaban kasa kan ayyukan yan bindiga da sace-sacen mutane saboda shugabannin da ke samun damar haduwa dashi suna tsoron fada masa gaskiya mai daci sannan sun gwammaci su dunga fadin “Ranka ya dade muna godiya da kokarin da kake yi,wallahi komai dai dai ne,ba matsala” ya rubuta a shafin Twitter.

A wani labarin kumaa, mun ji cewa Kungiyar dattawan arewa ta yi watsi da ikirarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa bai da hurumin sanya baki a rikicin da ke afkuwa tsakanin Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II saboda kundin tsarin mulkin kasar ya yi masa iyaka.

Kungiyar dattawan arewar ta ce a matsayin Buhari na jagoran al’umma, ba daidai bane ya ware kansa a gefe a lokacin da wani abu da ka iya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron wani yankin kasar ya kunno kai.

A cewar kungiyar aikata hakan ba zai zama yiwa kundin tsarin mulkin kasar shisshigi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel