Asibitocinmu sun koma wajen ajiye gawa shiyasa Buhari ya ke zuwa kasar waje
Fitaccen Lauya, Femi Falana SAN, ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su bukaci a inganta harkar kiwon lafiya a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Femi Falana ya bayyana cewa bai dace shugaba Buhari ya rika zuwa asibitocin kasar waje domin samun kulawa ba, amma an bar ‘Yan Najeriya a asibitocin gida.
Lauyan wanda ya yi kaurin suna wajen kare hakkin Bil Adama a kasar, ya misalta asibotcin Najeriya a gwamnatin shugaban kasa Buhari da dakunan ajiye gawa.
Falana ya bayyana cewa a lokacin da Buhari ya ke mulkin Soji, ya daure Dr. Beko Ransome-Kuti, don kurum ya bukaci gwamnati ta inganta asibitocin da ke Najeriya.
Gawurtaccen Lauyan ya yi wannan jawabi ne wajen wata laccar musamman da wata kungiyar kare Bil Adama ta shirya domin tunawa da Marigayi Beko Ransome-Kuti.
Farfesa Lai Olurode da Mai dakin Marigayin, Yemisi Ransome-Kuti sun halarci wannan lacca da aka yi mai taken ‘Shigar ‘Yan gwagwarmaya cikin tafiyar siyasa.”
KU KARANTA: Duk Afrika babu inda ake shan giya irin Najeriya - Bincike
“Lokacin da wannan shugaban kasar ya hau mulki a lokacin Soja a Disamban 1984, sai ya ce an maida asibitocin Najeriya sun koma dakunan ganin Likita kurum.”
“Wannan ya sa irinsu Beko Ransome-Kuti su ka dauka ya tabbatar da kukan da Likitoci su ke yi, bayan wattani shida da su ka ga babu canji, sai su ka tafi yajin aiki.”
“Sai aka kama Bekko, wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar NMA na farko. Aka garkame shi tare da shugaban NMA, Dr. Akpabio a kiri-kiri na watanni shida.”
“Mutumin da ya ce asibitoci sun zama wajen ganin Likita a 1984, shi ne shugaban kasa yau, saboda asibitoci sun zama dakin gawa, shiyasa ya ke zuwa ketare.”
A game da haramta Keke Napep da Babur a Legas, Falana ya ce laifin duk Buhari ne, wanda a 1984 ya soke kwangilar jirgin kasar gwamnatin Alhaji Lateef Jakande.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng