Festus Abiona: Hukumar EFCC ta yi nasarar cafke wanda FBI ta ke nema

Festus Abiona: Hukumar EFCC ta yi nasarar cafke wanda FBI ta ke nema

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta ce ta kama Festus Abiona wanda ake nema bisa zargin aikata laifuffuka.

Festus Abiona ya fada hannun EFCC ne bayan hukumar binciken kasar Amurka ta FBI ta jefa shi cikin wadanda ta ke zargi da damfarar Bayin Allah ta yanar gizo.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, shi ne ya bada wannan sanarwa a lokacin da ya ke zantawa da Manema labarai a Garin Ilorin a jiya Ranar Litinin.

“Abiona ya na cikin wadanda FBI ta shafe fiye da watanni takwas ta na neman sa a kan zargin damfarar mutane kafin dubunsa ta cika har aka kama shi.”

Mista Wilson Uwujaren ya ce an bi Abiona an damke shi ne har inda ya ke labewa. “Hukumar EFCC ta iya kama shi ne a Ranar Laraban makon jiya a gidansa.”

KU KARANTA: An kubutar da wasu Bayin Allah daga hannun Miyagun Barayi

Festus Abiona: Hukumar EFCC ta yi nasarar cafke wanda FBI ta ke nema
Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu
Asali: UGC

EFCC ta nuna cewa wanda ake zargi da zamban ya gina wani katafaren gida ne a Garin Arepo a jihar Ogun. Abiona ya damfari mutane da-dama a kasar Amurka.

“Daga ganin jami’an EFCC, sai ya jefa duka layukan wayar salulansa da na’urorin ATMs a cikin masai domin ya batar duk wata hujja da za a samu a hannunsa.”

“Duk da cewa tun da aka kama shi bai yi jawabi ba, za a gabatar da shi a kotu nan ba da dadewa ba.” Abiona ya dade ya na boye a gida saboda irin wannan rana.

“A Mayun 2015, wani ‘Dan damfara ya kutsa cikin asusun wasu Ma’aikata da su ka yi ritaya a Amurka, ya wawuri Dala miliyan 2.5.” Abiona ne da wannan aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel