Rundunar 'yan sanda ta bayyana masu goyon bayan sabuwar kungiyar 'yan ta'adda, "Ansaru"

Rundunar 'yan sanda ta bayyana masu goyon bayan sabuwar kungiyar 'yan ta'adda, "Ansaru"

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa bincikenta ya nuna mata cewa kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da takwararta ta Ansaru da sauran wasu kungiyoyin ta'addanci suna da magoya baya a tsakanin 'yan Najeriya.

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa (PPRO), DCP Frank Mba, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi.

Sai dai, jawabin nasa bai bayar da bayani a kan mutanen da suka gano cewa suna goyon bayan 'yan ta'addar ba.

Mba, wanda ya bayyana goyon bayan da kungiyoyin ke samu a matsayin babban abin takaici, ya ce rundunar 'yan sanda ta kama uku daga cikin mambobin kungiyar yayin wani farmaki da aka kai sansaninsu dake Kaduna ranar Laraba.

A ranar Laraba ne jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suka kai farmaki sansanin kungiyar Ansaru tare da kashe mambobin kungiyar 250, kamar yadda Mba ya sanar.

"Rundunar 'yan sanda ta kama wasu mambobin kungiyar Ansaru su uku a farmakin da aka kai sansaninsu da ke dajin Kuduru a karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana masu goyon bayan sabuwar kungiyar 'yan ta'adda, "Ansaru"
Frank Mba
Asali: UGC

"Mambobin kungiyar da aka kama sune kamar haka; Munkaila Liman Isah wanda aka fi kira da 'Babban Driver', mai shekaru 32, da Abdullahi Saminu wanda ake kira da 'Danmunafiki', mai shekaru 21, da kuma Aminu Isa, mai shekaru 22. Yanzu haka muna da mambobi kungiyar 8 a hannunmu.

DUBA WANNAN: Kallabi tsakanin rawuna: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka

"Abin takaici, bincikenmu ya nuna cewa akwai wasu 'yan Najeriya, musamman daga cikin 'yan kasuwa, da ke goyon baya da bawa kungiyar tallafi a sirrance.

"Babban sifeton rudnunar 'yan sanda (IGP) ya bukaci jama'a su kasance masu kishin kasa domin ta haka ne kawai hukuma zata samu nasarar yaki da 'yan ta'adda da kungiyoyin ta'addanci," a cewar Mba.

Mba ya kara da cewa jami'an rundunar 'yan sanda suna cigaba da bin sahun sauran mambobin kungiyar da suka tsere tare da bayyana cewa nan bada dadewa ba dukkansu zasu shigo hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel