Murna fal ciki yayinda hazikin dan sanda Abba Kyari ya samu sarauta a Maiduguri

Murna fal ciki yayinda hazikin dan sanda Abba Kyari ya samu sarauta a Maiduguri

- An ba shahararren jami’in dan sanda, Abba Kyari sarauta a Maiduguri

- A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairu, ya mika godiya ga majalisar masarautar kan zabarsa da suka yi bayan ganin cancantar bashi wannan sarauta.

- Kyari ya kuma yi godiya ga sarkinsa, Dr Mai Muckhtar Ibn Ali Gangarang, akan yardar da ya yi dashi

Rahotanni sun kawo cewa an ba haziki Abba Kyari, babban jami’in dan sanda day a kware wajen kama masu laifi da kuma warware manyan shari’ar ta’addanci da dama sarauta a Maiduguri.

Shine ya ayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairu, yayinda ya ke mika godiya ga basaraken, Dr Mai Muckhtar Ibn Ali Gangarang.

Baya ga shi, ya kuma mika godiya ga dukkanin majalisar masarautar Gujba kan yadda suka zabe shi cikin mutane da dama domin bashi wannan sarautar.

KU KARANTA KUMA: Wata bakuwar cuta ta bulla a jihar Benue, ta kashe mutum 15, sama da mutane 100 sun kamu

Koda dai ba a bayyana raar nadin sarautar ba tukuna, hazikin dan sandan ya ce ba da jimawa ba za a sanar da ranar bikin nadin.

A wani labari na daban, mun ji cewa wata kazamar rikici ta auku tsakanin jami’an hukumar yaki da fasa kauri, kwastam da yan kasuwa dake babbar kasuwar bajekoli ta ‘Trade Fair’ dake garin Ojo na jahar Legas, inji rahoton Aminiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a sanadiyyar wannan rikici an samu jama’a da dama da suka samu munanan rauni. Rikicin ya kaure ne a daidai lokacin da jami’an kwastam tare da Sojoji suka dira kasuwar da nufin kai samame tare da kwace haramtattun kayayyaki da aka shiga dasu kasuwar.

Hukumar kwastam ta bayyana cewa ta samu bayanin sirri dake nuna akwai tarin haramtattun kaya da aka shiga dasu kasuwar daga kasar Benin ta iyakar Najeriya da kasar na kan tudu dake garin Seme.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel