Abinda yasa rigingimu suka dabaibaye yankin arewa - Dogara

Abinda yasa rigingimu suka dabaibaye yankin arewa - Dogara

- Tsohon shugaban majalisar wakilai, Honarabul Yakubu Dogara, ya yi korafi a kan halin rashin tsaro a yankin arewa

- Dogara ya bayyana cewa yankin arewa bai taba shiga irin yanayin rudani ba kamar yadda yake ciki a yanzu

- Dan majalisar ya bayyana idan aka cire jihar Kwara da birnin tarayya, Abuja, babu jihar da bata fama da kalubalen tsaro

Yakubu Dogara ya bayyana cewa yankin arewacin Najeriya ya zama cibiyar rikici da rigingimu daban-daban tare da yin kira a nemo hanyoyin warware matsalolin da suka addabi yankin.

Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, a wurin wani taro a kan tsaro da wata cibiya (ARDP) ta shirya a Kaduna.

Ya bayyana cewar gazawar samun shugabaci nagari da zai hada kan al'umma tare da tabbatar da adalci ga kowa shine silar dukkan matsalolin tsaro da yankin arewa da Najeriya ke fama da su.

Abinda yasa rigingimu suka dabaibaye yankin arewa - Dogara
Yakubu Dogara
Asali: Twitter

A cewar Dogara, idan aka dauke jihar Kwara da Abuja, birnin tarayya, babu jihar arewa da bata fama da kalubalen tsaro.

DUBA WANNAN: Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya

"Muna fuskantar matsalolin da bamu taba ganin irinsu ba a tarihin yankin arewa. Mun zama makiyan juna, a saboda haka babu abinda zai hana mutuwa ta zama ruwan dare.

"Alamu sun dade da nuna wa amma muka yi burus dasu. Fasihin falsafa Sa'adu Zugur ya ankarar da mu cewa irin wannan lokacin yana zuwa, amma muki yi 'kunnen uwar shegu," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel