Valverde: ‘Dan wasa Lionel Messi ya samu sabani da Eric Abadal

Valverde: ‘Dan wasa Lionel Messi ya samu sabani da Eric Abadal

Abin da ba a saba ji ba ya faru a ‘yan kwanakin bayan nan, inda aka ji ‘Dan wasa Lionel Messi ya fito fili ya na caccakar Darektan Barcelona, Eric Abidal.

Tauraron ‘Dan kwallon ya maida martani ne ga Eric Abidal bayan ya zargi ‘Yan wasan kungiyar da rashin yin bakin kokarinsu kamar yadda ya dace a baya.

Abidal wanda shi ne Darektan harkar wasa ya ce ‘Yan kwallon Barcelona ba su ji dadin aiki da tsohon Kocinsu watau Ernesto Valverde wanda aka kora ba.

Messi wanda ba kasafai ya saba fitowa Duniya ya maida martani ko ya yi magana game da abubuwan da ba su shafi filin wasa ba, ya yi maza ya yi raddi.

Messi ya ce: “Gaskiya ba na son irin wannan lamari, amma ina tunani ya kamata kowa ya yi abin da ya dace, ya tsaya kan aikinsa, kuma su dauki nauyin aikinsu.”

KU KARANTA: Sabon Kocin Kungiyar Barcelona ya shiga kulob da kafar baya

Valverde: ‘Dan wasa Lionel Messi ya samu sabani da Eric Abadal
Abidal ya ce wasu 'Yan wasa ba su yi wa Valverde kwallo ba
Asali: Getty Images

‘Dan wasan ya cigaba da jawabi a shafinsa na Instagram ya na maidawa tsohon Abokin aikinsa martani: “Yan wasa su tsaya kan abubuwan da ya faru a filin kwallo.”

“Mu ke fara ganewa, mu ce ba mu yi kokari a filin kwallo idan wasa bai yi kyau ba.” Inji sa.

Tauraron ya kara da cewa: “Wadanda su ke da nauyin kula da harkar wasa, su maida hankali kan aikinsu, kuma muhimmin abu shi ne, su dauki nauyin aikin da su ka yi.”

‘Dan wasan na kasar Argentina bai tsaya nan ba, ya kuma nuna cewa idan Abidal ya na ganin wani ‘Dan wasa ba ya abin da ya dace, sai yi fito ya kama sunansa a fili.

“Ka kama suna, idan ba haka ba, ka na batawa kowa suna ne, kuma ka na yada jita-jitar karya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng