Trump ya soki Romney bayan ya goyi bayan a majalisa ta tsige Shugaban kasa

Trump ya soki Romney bayan ya goyi bayan a majalisa ta tsige Shugaban kasa

Idan mu ka koma siyasar Amurka, za mu ji cewa shugaba Donald Trump na kasar ya dura kan Sanata Mitt Romney a sakamakon kada kuri’a domin a tsige sa.

Sanata Mitt Romney shi ne kadai ‘Dan majalisar jam’iyyar Republican mai mulki da ya kada kuri’arsa domin a sauke shugaban kasa Donald Trump daga mulki.

A duk tsawon tarihin Amurka, wannan ne karon farko da aka samu ‘Dan majalisar jam’iyya ya na goyon bayan a tsige shugaban kasar da ya fito daga jam’iyyarsa.

Donald Trump ya yi amfani da shafinsa na Tuwita ya ya soki Romney:

“Da ace Romney wanda ya sha kashi, ya yi amfani da irin zimmar yadda ya ke taso ni a gaba wajen tika Barack Obama da kasa, da watakila ya lashe zabe.”

KU KARANTA: Abubuwan da su ka hana a iya tsige Trump a Majalisa

Trump ya na magana ne game da takarar da Romney ya yi da Abokin hamayya Obama a 2012, inda ya sha kashi, amma kuma yanzu ya hurowa na gidansa wuta.

Shugaban ya sake musanya zargin cewa ya aikata ba daidai ba kamar yadda majalisar wakilai ta zarge shi, inda ya sake fadawa Sanatan ya karanta rahoton binciken.

Shi ma Donald Trump Jr., wanda ‘Dan cikin shugaban kasar Amurka ne, ya soki Romney, har ya yi masa albashir da cewa ba zai taba zama shugaban kasar Amurka ba.

Trump Jr. ya yi kira ga jam’iyyar Republican mai mulki a Amurka da ta kori Mitt Romney daga cikin ‘Ya ‘yanta, a dalilin hada-kai da ya yi da ‘Yan adawa a majalisa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel