Al-Mustapha: Sharri ake yi wa Abacha, ni ma an nemi in yi wa Buhari kazafi

Al-Mustapha: Sharri ake yi wa Abacha, ni ma an nemi in yi wa Buhari kazafi

Manjo Janar Hamza Al-Mustapha ya karyata zargin da ake jifan tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, da shi na cewa ya saci makudan dalolin kudi.

Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa a lokacin da Sani Abacha ya dare kan mulki, abin da Najeriya ta mallaka a asusun kudin kasar waje bai da yawa.

A cewar Al-Mustapha, Abacha ya gaji abin da bai kai Dala miliyan 200 ne a asusun kudin kasar waje, amma kafin ya bar mulki ya tara dala tara da ‘yan kai.

Tsohon babban jami’in da ke kula da tsaron Sani Abacha a lokacin da ya ke kan mulki ya ce shugabannin da aka yi a baya ne su ka sace dukiyar Najeriya.

Tsohon Sojan kasar ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi da safiyar Ranar Alhamis, 6 ga Watan Fubrairun 2020, a gidan rediyon VOA Hausa.

KU KARANTA: Abubuwan kwarai da Sani Abacha ya yi a lokacin ya na mulki

Al-Mustapha: Sharri ake yi wa Abacha, ni ma an nemi in yi wa Buhari kazafi
Abacha ya bar $9.7b a asusun kudin kasar waje inji Al-Mustapha
Asali: UGC

Hamza Al-Mustapha wanda ya yi zaman gidan yari na shekara da shekaru, ya ce an bukaci ya yi wa Muhammadu Buhari irin wannan kazafi da ake yi wa Abacha.

Al-Mustapha ya ce a baya an tursasa masa ya fito ya ce an saci kudin gwamnati a ma’aikatar PTF ta rarar mai da Buhari ya jagoranta a lokacin gwamnatin sojin.

A na sa ra’ayin, da za a fito a yi yaki da rashin gaskiya da gaske, da an kama mutane da yawa an daure a Najeriya. Al-Mustapha ya ce ba da gaske ake yin lamarin ba.

Kwanan nan mu ka ji cewa kasar Amurka za ta dawowa gwamnatin Najeriya da wasu fam Dala Miliyan 308 da aka ce an wawura a lokacin Janar Sani Abacha.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel