Amurka: Abin da ya sa Majalisar Dattawa ta iya wanke Donald Trump

Amurka: Abin da ya sa Majalisar Dattawa ta iya wanke Donald Trump

Bayan kusan makonni biyu ana ta kai ruwa rana, Sanatocin kasar Amurka sun fitar da matsaya game da batun tsige shugaba Donald Trump daga kan mulki.

BBC ta kawo dalilai hudu da su ka taimakawa shugaban kasa Donald Trump wajen tsallake yunkurin tsige shi daga kan kujerar mulki a Ranar Larabar nan.

Ga wasu daga cikin wadannan dalilai:

1. Farin jinin Donald Trump

Farin jinin Donald Trump ya yi aiki a majalisa inda alkaluma su ka nuna 94% na ‘Yan jam’iyyarsa su na tare da shi. Sai kuma wasu su na ganin cewa ba kaunar Trump ta jawo masa wannan ba, ana dai ganin cewa bai yi abin da ya cancanci a tsige shi daga mulki ba ne.

2. Rinjayen Jam’iyya mai mulki a Majalisar dattawa

Jam’iyyar ‘Republicans’ wadanda su ke da rinjaye a majalisar dattawa sun taimakawa Donald Trump. A halin yanzu ‘Yan jam’iyyar Trump ne su ke da rinjaye da mutum 53-47. Mafi yawan ‘Republicans’ sun marawa Trump baya face irinsu Sanata Mitt Romney.

KU KARANTA: Majalisar Dattawan Amurka ba su samu Shugaba Trump da laifi ba

Amurka: Abin da ya sa Majalisar Dattawa ta iya wanke Donald Trump
Donald Trump zai cigaba da mulki har zuwa karshen wa'adinsa
Asali: Depositphotos

3. Kuri’un Sanatocin da ake bukata

Wani abu da ya yi tasiri wajen wanke Donald Trump daga laifi shi ne akwai bukatar kaso biyu-cikin-uku na Sanatocin Amurka kafin a iya tsige shugaban. Wannan na nufin Sanatocin hamayya su na neman karin mutane 20 su samu kuri’a 67, a karshe su ka gaza.

Yanzu dai Donald Trump ya dawo da hankalinsa wajen neman tazarce, kuma Magoya bayansa sun tara masa makudan kudi domin ganin ya sake samun nasara a bana.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sanatan 'Republican' guda ne kawai ya zabi a tsige Donald Trump, wannan Sanata shi ne Mitt Romney wanda ya taba takara da Obama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel