EFCC: Saboda na taba wasu Barayin mai Jonathan ya kore ni – Inji Waziri

EFCC: Saboda na taba wasu Barayin mai Jonathan ya kore ni – Inji Waziri

Farida Waziri, wanda ta rike kujerar shugabar hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta bayyana dalilin da ya sa ta bar ofis.

Misis Farida Waziri ta shugabanci hukumar ta EFCC na wani lokaci kafin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tsige ta, ta fito ta bada labarin abin da ya faru.

The Nation ta rahoto Waziri ta na cewa yunkurin kama wasu Barayin mai ne ya jefa ta a rami, wannan bincike da ta fara ya sa aka kira ta daga fadar shugaban kasa.

Waziri ta ki biyawa wadannan mutane bukatarsu, inda ta cigaba da gudanar da bincikenta, wannan ya yi sanadiyyar da ta rasa aikinta a gwamnatin Jonathan inji ta.

Tsohuwar shugabar ta EFCC ta tuna yadda wasu manya a gwamnatin Jonathan su ka ba ta shawarar ta roki shugaban kasa a lokacin da ake faman yunkurin tsige ta.

KU KARANTA: Sanatocin Amurka sun wanke Shugaban kasa Donald Trump

EFCC: Saboda na taba wasu Barayin mai Jonathan ya kore ni – Inji Waziri
A karshen 2011, Jonathan ya kori Farida Waziri daga EFCC
Asali: Depositphotos

A cewar Farida Waziri, ba ta bada hakurin a bar ta a kan kujerarta ba, kuma ba ta bada kudin yakin neman zabe a lokacin da Jonathan ya ke neman takara a zaben 2011.

Rahotanni sun nuna cewa bayan wadannan, daga cikin abin da ya hada Waziri fada da gwamnatin PDP a lokaci shi ne kin bada gudumuwa domin tazarcen Jonathan.

Har ila yau, ta bayyana cewa daga cikin dabarar da aka yi na korarta daga aiki shi ne aka yi mata tayin wani mukamin dabam, haka zalika wannan dabara ba ta yi masu aiki ba.

An samu duk wadannan bayanai ne a cikin littafin da Farida Waziri ta rubuta mai suna Farida Waziri, One Step Ahead inda ta soki gwamnatin shugaba Dr. Goodluck Jonathan.

A na ta labarin, ta ce ta shiga matsala ne tun bayan rasuwar Umaru Yar’Adua, domin shi ne ya tsaya tsayin-daka wajen ganin ya yaki barayi, sabanin Magajin na sa, a cewarta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel