Rundunar 'yan sanda ta kubutar da mutane 26 daga hannun masu garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sanda ta kubutar da mutane 26 daga hannun masu garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da cewa ta kubutar da mutane 26 da masu garkuwa da mutane a Dugun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, shine ya sanar da hakan yayin wani taro da manema labarai da ya kira ranar Laraba a Katsina.

Isah, mai mukamin SP, ya sanar da cewa akwai Mata 8 da Maza 18 daga cikin mutanen da suka kubutar.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutane sun sace mutanen ne ranar 6 ga watan Janairu yayin da 'yan ta'adda kimanin su 50 suka kai hari kauyen Badna-Buruku da ke karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna.

Isah ya kara da cewa 'yan bindigar sun sace mutanen zuwa wani jeji da ke jihar Zamfara.

A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun nemi miliyan daya a matsayin kudin fansa a kan kowanne mutum daga cikin mutanen 26 da suka sace tare da yin barazanar cewa zasu kashe duk wanda ba a biya masa kudin ba.

Ya bayyana cewa jami'an rundunar 'yan sanda da ke sintiri sun ci karo da mutanen suna gararamba a daidai wani daji da ke kauyen Dungun Muazu a karamar hukumar Sabuwa.

Kakakin ya bayyana cewa sun mika mutanen asibitin rundunar 'yan sanda da ke Katsina domin a duba lafiyarsu kafin daga bisani a sada su ga danginsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel