Qaw’mane Wilson zai yi zaman kurkuku bayan ya sa an kashe tsohuwarsa a 2012

Qaw’mane Wilson zai yi zaman kurkuku bayan ya sa an kashe tsohuwarsa a 2012

Mun samu labari cewa wani Alkali ya yanke hukunci a daure Mawakin nan kasar Chicago, Qaw’mane Wilson, a gidan yari na tsawon shekaru 99.

Rahotanni sun zo mana cewa an samu Qaw’mane Wilson da laifin biyan wani kwararren ‘Dan bindiga kudi domin ya taimaka ya kashe tsohuwarsa.

A Ranar karshe a Watan jiya Alkali ya daure Mawakin a gidan yari na tsawon shekara 99 a sakamakon kama shi da laifin kisan kai a shekarar 2013.

Watanni kadan bayan mutuwar tsohuwarsa, aka ga Wilson a cikin dambareriyar motar Ford Mustang. Wannan ya sa Mawakin ya kara shigowa gari.

Mawakin mai tasowa a Duniya ya kan rabawa Jama’a kudi cikin facaka saboda ya samu farin jini a cikin Mawaka bayan ya yi nasarar kashe Mahaifiyarsa.

KU KARANTA: Wani 'Dan Sanda ya rataye kansa har lahira a ofis

Qaw’mane Wilson zai yi zaman kurkuku bayan ya sa an kashe tsohuwarsa a 2012
Wilson ya sa wani ya kashe tsohuwarsa don ya ci gado
Asali: Twitter

An rahoto cewa Tauraron ya kan watsa kudi a iska domin Masoyansa su shiga wawaso. Wannan facaka ta na cikin yadda Wilson ya rika kashe dukiyar gadon.

Lauyoyi sun bayyana cewa Wilson ya shiga barna da dukiyar da Mahaifiyarsa ta bar masa ne domin dama can shi ya kawo shawarar yadda za a hallaka ta.

Abin da Yolanda Holmes ta bar wa Wilson sun kai fam Dala $90, 000 (a kudin Najeriya N32, 715, 000). Wannan ya sa aka rika ganinsa a shaguna ya na holewa.

Jaridar Chicago Sun-Times ta bayyana cewa kotu ta yankewa asalin wanda ya kashe wannan Baiwar Allah, Eugene Spencer, hukuncin daurin shekaru 100.

Alkali Stanley Sacks ya yi mamakin yadda mutum zai sa a dauki ran Mahaifiyarsa saboda neman Duniya. Wilson dai ya fadawa kotu cewa ya na kaunar Uwarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel