Wuta ta kama kamfanin wutar lantarkin IBEDC a Garin Ibadan

Wuta ta kama kamfanin wutar lantarkin IBEDC a Garin Ibadan

Kamfanin raba wutar lantarkin Najeriya na IBEDC watau Ibadan Electricity Distribution Company, Ibadan ya na ci da wuta a halin yanzu.

Da safiyar Ranar Laraba, 5 ga Watan Fubrairun 2020, mu ka samu wani labari maras dadi cewa gobara ta rutsa ginin wannan kamfanin lantarki.

Jaridar The Nation ce ta kawo rahoto cewa an ga wuta ya na ci a wannan gini da ke Yankin Ayede a Akinyemi a babban birnin Oyo watau Ibadan.

Kawo yanzu da kimanin karfe 10:00 da mu ke tattara wannan rahoto, wutar ta na cigaba da ci. Ba a samu labarin abin da ya jawo wannan gobara ba.

KU KARANTA: Jami'i ya kashe kansa da kansa a ofishin 'Yan Sanda

Wuta ta kama kamfanin wutar lantarkin IBEDC a Garin Ibadan
Wasu Ma'aikatan kamfanin IBEDC kwanakin baya a wajen taro
Asali: UGC

Haka zalika ba a samu labarin irin barnar da wannan gobara ta yi wa ofishin kamfanin wutan da sauran gine-ginen da ke makwabtaka da wurin ba.

A Ranar Talatan makon nan an samu irin wannan gobara idan ba ku manta ba. Wuta ta kama a kan babban titin Akala da ke Garin na Ibadan.

Wutan da ta fara daga cikin wasu shagunan haya ta barko zuwa bakin titi bayan ya yi ta’adi. Ana yawan samun matsalar gobara a cikin lokacin sanyi.

Za mu kawo maku labarin yadda ake ciki idan rahoto ya zo mana. Har yanzu ana fama da matsalar rashin isassun kayan kashe gobara a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel