Ka da ‘Yan siyasa su sake su batawa kotu suna – inji Bola Tinubu

Ka da ‘Yan siyasa su sake su batawa kotu suna – inji Bola Tinubu

A Ranar Litinin dinnnan ne Jagoran jam’iyyar APC a Kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira da a daina bata bangaren shari’a.

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa a tsarin farar hula, dole a ba masu kula da harkar shari’a girmansu, tare da rike su da darajar da aka sansu da ita.

Fitaccen ‘Dan siyasar ya bada shawarar cewa a tsari na damukaradiyya, ya zama dole a bi dokar kasa da hukuncin kotu ko da bai yi wa jama’a dadi ba.

Tinubu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya halarci zaman karshen da kotun koli ta shiryawa Alkalinta, Amiru Sanusi, wanda ya yi ritaya daga aiki.

Alkali Amiru Sanusi ya ajiye aikinsa a babban kotun kasar ne bayan ya cika shekaru 70 a Duniya. Doka ta yi wa Alkalai tanadin ritaya daga aiki a shekara 70.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta karyata Shehu Sani bayan an bada belinsa

Ka da ‘Yan siyasa su sake su batawa kotu suna – inji Bola Tinubu
Wasu Jiga-jigan PDP su na yi wa kotun koli zanga-zanga kwanaki
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na Legas ya ke cewa: “Tun da Najeriya ta zabi mulkin farar hula, ya zama dole ayi biyayya sau-da-kafa da dokar kasa da tsarin mulki.”

“Eh. Wasu za su yi nasara a gaban kuliya, wasu za su rasa kara a kotu. Amma ana ganin gaskiya da adalci da ya-kamata a shari’ar Alkalai.” Inji Tinubu.

“Wannan mu ka daukarwa kanmu da mu ka zabi aiki da tsarin damukaradiyya. Ka da mu batawa Alkalai suna kawai don hukunci bai yi mana dadi ba.”

“Rayuwa ta na da wahala. Hukuncin daidai sai Ubangiji. Idan ka fahimci kotu ta yi kuskure a shari’a, sai ka yi hakuri, ba kullum ake kwana a gado ba.”

Kwanaki wasu daga cikin ‘Yan jam’iyyar PDP sun yi zanga-zanga bayan Alkalai sun tsige gwamnan Imo, inda su ka mika mulki ga Jam’iyyar APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel