Kurunkus: Nathaniel Samuel ya fadi sunan wacce ta tura shi cikin coci da bam

Kurunkus: Nathaniel Samuel ya fadi sunan wacce ta tura shi cikin coci da bam

Mutumin da aka kama da bam a cikin coci da ke Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna mai suna Nathaniel Samuel mai shekaru 30 ya bayyana cewa wata mata ce ta bashi ababen fashewar.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa wata mata ce mai suna Grace ta ba shi jakar kunshe da kayan a bikin da ya halarta a Sabo, ranar Asabar. Ya ce a tunaninsa abin kawata waje ne amma sai da 'yan sanda suka kama shi ne ya san cewa abu mai fashewa ne a ciki.

Ya ce aikin shi shine kawata waje kuma abinda ya shigar da shi cocin kenan.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama Nathaniel ne a ranar Lahadi bayan da aka zargesa da dasa bam a cikin cocin Living Faith da ke Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna.

Bayan yunkurinsa bai cimma nasara ba a cocin, rahotanni sun dinga yawo cewa ba Kirista bane, Musulmi ne.

DUBA WANNAN: Turai Yar'adua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Bayan 'yan sanda sun kama shi sun masa tambayoyi, sun gabatar da shi gaban manema labarai domin ya yi musu bayanin ko shi wanene da abinda ya kai shi cocin, ya fara da cewa:

"Suna na Nathaniel Samuel Kolik, dan asalin jihar Bauchi. Na tafi cocin Living Faith da ke Sabo misalin karfe 8 na safe domin hallarton wa'azi na farko. A lokacin da na ke zaune a cikin cocin ina sauraron hudubar da fasto ke yi, kwatsam sai ciki na ya fara murduwa.

"Hakan ya sa na shiga ban daki, na shigo cocin dauke da jaka da kaya na ciki saboda a kwana guda kafin in zo cocin na hallarci wani taro a Unguwan Boro a Sabo."

Nathaniel ya cigaba da cewa 'yan sanda sun duba jakarsa sun gano cewa ba ababen fashewa bane, kayan wasan wuta ne sai dai Kakakin 'yan sanda Yakubu Sabo ya masa raddi nan take inda ya ce inda ya canja maganarsa ya kuma amsa cewa ababen fashewa ne.

"Ainihin abin da ya faru shine wata mata mai suna Grace ce ta bani kayan a wurin taron da na halarta, da ta bani kuma ban san mene ke ciki ba har sai bayan da 'yan sanda suka kama ni suka bincika," in ji Nathaniel.

Amma kuma wanda ake zargin ya sanar da manema labarai cewa sunansa Nathaniel ba Mohammed Nasiru Sani ba. Ya kamata ace ya zama fasto don ya halarci makarantar Leadership and Training Institute of the Living Faith Church Worldwide, Word of Faith Bible Institute.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel