Ekiti: Barawon waya zai shafe shekaru 7 a cikin gidan yari

Ekiti: Barawon waya zai shafe shekaru 7 a cikin gidan yari

Wata babbar kotu da ke jihar Ekiti ta yankewa wani mutumi hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan kurkuku a sakamakon kama shi da laifin sata.

Wannan Mutumi ya burma gidan jama’a ya shiga ya yi sata. Sunan wannan Mutumi da aka kama Akin Afolarin kamar yadda mu ka samu labari dazu.

Alkali mai shari’a Lekan Ogunmoye, shi ne ya saurari wannan kara da gwamnati ta shigar kwanakin baya a kotun na sa da ke zama a Ado-Ekiti.

Kwamishinan shari’a na jihar Ekiti, Olawale Fapohunda, shi ne ya jagoranci wannan kara a gaban kotu kamar yadda rahotanni su ka bayyana mana.

Akin Afolarin ya shiga gidan jama’a ba tare da izni ba, sannan kuma ya sace wayoyin salula biyu. Bayan an yi bincike ne, aka kama wannan Mutumi.

KU KARANTA: Sin ta gina katafaren asibiti a cikin mako guda saboda annoba

An gano wayar ne a hannun wani Ma’aikacin banki, wanda ya ce ya saye wayar a hannun wani Seun. Shi kuma Seun ya saye wayar wajen Afolarin.

Mista Afolarin shi ne wanda a karshe kotu ta samu da laifin sace wayoyin tun farko, har ya saida su a kasuwa, kafin a iya gano ta a hannun wasu dabam.

Afolarin ya yi ikirarin cewa ya saye wayar ne a hannun wani Malam Aminu. Amma a karshe ya gaza kawo wannan Mutumi da ya kira a gaban kotu.

A dalilin gaza kawo shaidansa, kotu ta samu Akin Afolarin da laifin sata. Alkali ya kuma daure shi da laifin shiga gidan mutane ba tare da izninsu ba.

Alkali Ogunmoye ya ba wanda aka kama da laifi damar biyan tara na N70, 000. Muddin wannan Barawo ya biya wannan kudi, ba zai yi zaman kaso ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng