An kama wata Ma’aikaciya da ke damfarar masu neman aiki a Kwara

An kama wata Ma’aikaciya da ke damfarar masu neman aiki a Kwara

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta kama wata Mata da zargin damfarar Bayin Allah a jihar Kwara.

Jami’an hukumar da ke reshen Ilorin, sun yi ram da Olajumoke Rhoda Oyawoye bisa laifin cewa ta na karbar kudi da sunan za ta ba mutane aiki.

Misis Olajumoke Oyawoye ta kan yaudari Matasa da ke neman abin yi cewa ta na da hanyar sama masu aiki da gwamnatin tarayya ko jiha.

Wannan Mata babbar jami’ar gwamnatin jihar Kwara ce wanda ta kai mataki na 14 na aiki a ma’aikatar kudi kamar yadda mu ka samu labari.

Olajumoke Oyawoye ta karbi kudi da su ka kai Naira miliyan uku wajen jama’a duk da karyar za ta kawo masu takardun samun aiki da gwamnati.

KU KARANTA: Watakila za a sallami Ma'aikatan N-Power - Ministar Najeriya

Wannan Mata ta samu kanta cikin matsala ne a sakamakon karar ta da Solomon Moronfoye da Salako Olalekan Abdulgafar su ka kai ofishin EFCC.

Moronfoye ya fadawa hukumar EFCC cewa ya hadu da wannan Mata a wani coci a Garin Offa, inda ta masa alkawarin samo masa aikin gwamnati.

“Ta fada mani cewa kudin samun aikin gwamnatin jiha N250, 000 ne, yayin da kuma na samun aiki a gwamnatin tarayya ya ke N350. 000” Inji sa.

Mista Moronfoye ya ce a haka ya ba Olajumoke Oyawoye Naira miliyan biyu domin a ba wasu mutane aiki, kuma ta fada masa cewa an ba su aikin.

EFCC ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da aka samu wajen wannan Mata akwai takardun CV da na samun aiki. Nan gaba kadan za a kai ta kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel