Doyin Okupe ya yi magana game da salon Gwamnatin Shugaba Buhari

Doyin Okupe ya yi magana game da salon Gwamnatin Shugaba Buhari

Dr. Doyin Okupe wanda ya yi aiki a karkashin shugabannin kasa; Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan ya yi magana game da kamun ludayin gwamnatin APC mai mulki.

Doyin Okupe ya nuna cewa gazawar gwamnatin shugaba Buhari ta sa ana yawan daura laifi ga jam’iyyar PDP. A cewarsa, APC ba ta iya cika duk alkawuran da ta dauka ba.

A game da batun da kungiyar CAN ta ke yi na cewa ana gallazawa Kiristocin Arewa, Okupe ya nuna cewa ya yarda da wannan magana, kuma tun ba yau ba, haka ake fama.

“Ba yau aka fara ba, an dade a haka. Idan ka ji ainihin abubuwan da ke faruwa da Kiristoci a Arewa, za ka san su na shan wahala sosai. An dauke su ‘Yar bowa a cikin kasar.”

Dr. Okupe ya ke cewa: “Abin kunya ne ga Najeriya, bai kamata a dauki wannan cin kashi ba, kuma bai kamata wannan ya rika faruwa a al’umma a irin wannan zamani ba.”

KU KARANTA: Mutane 40 sun shiga hannun ‘Yan Sanda saboda Acaba a Legas

Doyin Okupe ya yi magana game da salon Gwamnatin Shugaba Buhari
Okupe ya ce yadda aka hallata shari'a bai kamata a hana Amotekun ba
Asali: UGC

A game da Dakarun Amotekun da aka kirkira a Kudancin Najeriya, Okupe ya ace wannan bai kamata ya zama wani abin tada jijiyoyin wuya ba, domin su na da gindin zama.

‘Dan adawar ya na ganin akwai hannun ‘Yan Arewa a lamarin. “Arewa za ta dauki alhaki idan aka samu matsala game da Amotekun, manyan Arewa ya kamata a kama da laifi.”

Haka zalika a game da batun rabon mukami, ‘Dan adawar ya koka da cewa ba a yin adalci, sannan kuma ya ce ya kamata Buhari ya rika la’akari da cancanta wajen raba mukamai.

Tsohon Hadimin ya na cikin wadanda su ka rika kira a canzawa PDP zani saboda jama’a su sake mata kallo, Okupe ya ce zai cigaba da kokarin ganin an ci ma wannan manufa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel