Harkar fim tamkar kabari ce, idan an shiga ba a fita - Jamila Gamdare

Harkar fim tamkar kabari ce, idan an shiga ba a fita - Jamila Gamdare

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar Kannywood wacc ta fi karfi a fina-finan barkwanci na Dan Ibro, Jamila Gamdare ta yi sharhi kan rashin ganinta a cikin fina-finai tun bayan rasuwar ubangidan nata.

A wancan lokacin babu wata jaruma da ta yi fice a finafinan Ibro bayan rasuwar Hussaina Gombe (Tsigai) kamar ta. Hakan ne ya sa aka riƙa yi mata laƙabi da Sarauniyar Camama, saboda irin rawar da ta riƙa takawa a finafinan bakwancin, waɗanda ake kira da camama.

To sai dai tun daga rasuwar Ibro sai tauraruwar jarumar ta yi ƙasa, aka daina ganin ta.

Harkar fim tamkar kabari ce, idan an shiga ba a fita - Jamila Gamdare
Harkar fim tamkar kabari ce, idan an shiga ba a fita - Jamila Gamdare
Asali: Twitter

A hira da jarumar ta yi da mujjalar Fim game da matsayarta a harkar fim a yanzu, sai ta ce: "To, ina nan a cikin harkar fim, ban bar ta ba kuma ba ni da shirin barin ta domin ita harkar da ita aka san ni a duniya, duk wani abu da na samu albarkacin harkar fim ne, domin yanzu ko aure na yi to darajar fim ta sa aka aure ni. Don haka ina cikin harkar fim har yau har gobe."

Dangane da rashin ganin ta da ba a yi a cikin finafinai kuwa, ta ce: "To ba a gani na ne, amma lokaci-lokaci ina yin fim.

"Kuma ka san harkar fim ta na da faɗi, ba sai ka na aktin ka ke ɗan fim ba. Don haka ko ban yi aktin ba ina yin wasu harkoki a cikin masana'antar, kamar waƙa da ɗaukar nauyin fim da sauran su.

"Don haka ina cikin harkar fim ban fita ba, domin ita harkar fim kamar kabari ce, idan an shiga ba a fita, kawai sai dai fatan cikawa da imani."

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta karrama hazikan sojoji 37 a arewa maso gabas

Game da yadda take ganin harkar fim a yanzu, jarumar ta ce: "To idan ma akwai dalilin da zan ce shi ya sa ba a gani na, sai dai in ce shi ne yanayin yadda harkar ta ke a yanzu, domin yanayin da masana'antar ta samu kan ta a ciki shi ne ya ɓoye kowa, don haka mutane su na bin wasu hanyoyi wanda za su rufa wa kan su asiri, amma dai harkar fim ɗin dai ita ce ta zame mana jagora, duk inda mu ka je to cikin ta za mu dawo.

Daga ƙarshe jarumar ta yi fatan harkar fim za ta dawo cikin hayyacin ta. A cewar ta; "Halin da harkar fim ta ke ciki a yanzu, sai dai addu'ar Allah ya kawo mana mafita."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel