Al’amarin tsaro a arewa maso gabas na kara tabarbarewa – Sanata Ndume

Al’amarin tsaro a arewa maso gabas na kara tabarbarewa – Sanata Ndume

- Sanata Ali Ndume, ya koka kan halin da ake ciki a arewa maso gabas cewa abubuwa na kara tabarbarewa a kullun

- Ndume ya kuma yi korafi kan yawan kashe-kashe da rikice-rikice a mazabarsa

- Sanatan ya ce ya kamata gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta farka game da hakkin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyi

Dan majalisa mai wakiltan Borno ta Kudu a majalisar dokokin tarayya, Sanata Ali Ndume, ya koka kan halin da ake ciki a arewa maso gabas cewa abubuwa na kara tabarbarewa a kullu yaumin.

Da yake magana a wata hira da Channels Television a shirin Sunday Politics, Ndume ya nuna bakin kan dawowar yan ta’addan Boko Haram da ISWAP wadanda ke karuwa.

Ndume wanda ya kasance Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, ya kuma yi korafi kan yawan kashe-kashe da rikice-rikice a mazabarsa.

A cewarsa, kwanan nan yan bindigan suka kai hari kananan hukumomin Askira da Damboa da ke jiharsa inda suka kashe wasu mutane sannan suka tsere da kayayyakin abinci da sauran kayan amfani.

Al’amarin tsaro a arewa maso gabas na kara tabarbarewa – Sanata Ndume
Al’amarin tsaro a arewa maso gabas na kara tabarbarewa – Sanata Ndume
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa jami’an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar mayar da martani ga harin a kan lokaci ta hanyar dakile harin yan ta’addan, said a mutane suka tsere domin neman mafaka saboda tsoro.

Da yake ci gaba da magana, dan majalisar ya ce sabon harin da aka kai jihar ya zo ne a daidai lokacin da mutane ke ganin alamun dawowar zaman lafiya cewa yawan hare-hare ya ragu.

Ya bayyana cewa a makon da ya gabata, bama-bamai biyu aka dana a wani masallaci a Gwoza, da kuma harin da aka kai Muno, kusa da Maiuguri a makon da ya gabata.

Koda dai Ndume ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, yana so gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta farka game da hakkin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyi.

KU KARANTA KUMA: Bayan watanni 10 a hannu, dan bautan kasa kirista ya bayyana dalilin da yasa yake son cigaba da zama tare da Boko Haram

Da aka tambaye shi kan martaninsa ga kira da Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Eyinanya Abaribe ya yi kan Shugaba Buhari ya yi murabus sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin tsaron kasar, Ndume ya ce kiran bai da wani alfanu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel