Gwamnati ba za ta zare tallafi mai ba sai an gyara matatu – Sanata Olamilekan

Gwamnati ba za ta zare tallafi mai ba sai an gyara matatu – Sanata Olamilekan

Mun ji cewa Sanatocin Najeriya sun bayyana cewa babu maganar cire tallafin da gwamnati ta sa wajen sayen man fetur sai nan da wani lokaci.

‘Yan majalisar dattawan sun nuna cewa har sai lokacin da matatun gwamnati su ka dawo aiki sannnan za a iya cire tallafin man fetur a Najeriya.

Wannan bayani ya sha ban-ban da matsayar da Majalisar ta cin ma a shekarar da ta wuce na 2019 game da yadda ake gudanar da sha’anin tallafin mai.

A shekarar bara, Sanatoci sun koka da cewa babu gaskiya wajen biyan kudin tallafin man fetur, ganin irin kudin da ake biyan masu shigo da mai kasar.

A yanzu Majalisar Dattawa ta bakin shugaban kwamitin kudi, Sanata Solomon Olamilekan, ta ce akwai bukatar a shawo karshen wannan dambarwa.

KU KARANTA: Yadda aka rika kara farashin mai tun daga Kobo 6 zuwa N141

Gwamnati ba za ta zare tallafi mai ba sai an gyara matatu – Sanata Olamilekan
Sanata Olamilekan ya ce a gyara matatun mai kafin a cire tallafi
Asali: Twitter

Da ya ke zantawa da ‘Yan Jarida a Ranar Asabar, Solomon Olamilekan, ya ce: “Mun yarda cewa dole mu samu hanyar kawo karshen batun tallafin mai.”

“Ina ganin an yi amfani da kudin da ake kashewa wajen tallafin man fetur a cikin kasafin kudi. Sai kuma mu fahimci halin da ake ciki a nan da can.”

Sanatan na APC mai wakiltar Legas ya ce: “Mu na bukatar mu gyara matatunmu su fara aiki. Ya kamata su fara aiki kafin mu fara tunanin cire tallafi.”

“Domin idan mu ka zare tallafi gaba daya nan-take, za mu jefa ‘Yan Najeriya cikin wani irin mawuyacin hali da ba zai yi kyawun ji ba” Inji Sanatan.

‘Dan majalisar ya kuma gargadi gwamnati su guji kara haraji a jihohinsu, tare da sanar da cewa kashi 80% na kudin VAT zai shigo asusun jihohi ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel