Uche Maduagwu: Kusan duk ‘Yan wasa da bin Maza su ke sayen manyan gidaje

Uche Maduagwu: Kusan duk ‘Yan wasa da bin Maza su ke sayen manyan gidaje

Fitaccen ‘Dan wasan nan na Nollywood, Uche Maduagwu, ya fito ya yi magana game da halin da ake ciki a harkar fina-finai a Najeriya.

Uche Maduagwu ya bayyana cewa Taurarin Matan wasan kwaikwayo su ka san samu kudinsu ne ta hanyar lalata da su ke yi a waje.

Mista Maduagwu wanda ba yau ya fara yin baram-barama ba, ya yi wannan magana ne a kan shafinsa na Instagram a Ranar Asabar.

An dade ana zargin wadanda ke cikin masana’antar Nollywood da lalata saboda samun abin Duniya tun kafin maganar Maduagwu.

‘Dan wasan ya ke cewa wasu Taurari su kan tafi Birnin Dubai a kasar UAE su yi ta zaman kansu, su samu makudan miliyoyin kudi.

KU KARANTA: Na zabi na cigaba da zama a hannun Boko Haram - Tsohon 'Dan NYSC

Uche Maduagwu: Kusan duk ‘Yan wasa a sanadiyyar bin Maza su ka saye gida
Shararren ‘Dan wasa Uche Maduagwu ya zargi 'Yam fim da lalata
Asali: UGC

Tauraron ya ke cewa irin wadannan Taurari su kan fake da inuwar wasan kwaikwayo, su na cewa da shirin fim su ka yi kudi.

A cewarsa, wadannan ‘Yan wasan kwaikwayo su kan yi lalata da ‘Yan siyasa a Dubai, sai su dawo Najeriya su saye manyan gidaje.

Matashin ‘Dan wasan ya ke cewa Taurarin su na yaudarar jama’a ta hanyar nuna masu kamar su na cire kudi ne a bishiya a Nollywood.

A jawabinsa, ya ba masu wannan aiki shawarar su daina yin abin da zai sa wasu ‘Yan wasa za su ji kamar ba su bakin kokarinsu.

Duk da wannan kudin goro da ‘Dan wasan ya yi wa ‘Yan fim, bai fadi sunan wadanda ake yin lalata da su a gidan Nollywood ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng