Kano: Babu rikicin komai tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi II – Inji Kwamishinan labarai

Kano: Babu rikicin komai tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi II – Inji Kwamishinan labarai

Mun samu labari cewa gwamnatin jihar Kano ta musanya hannunta a cikin sabon binciken da hukumar yaki da rashin gaskiya ta ke yi wa masarautar Birnin Kano.

Kwanan nan ne aka ji cewa hukuma ta na zargin masarautar Muhammadu Sanusi II da badakalar saida filayen gwamnati ba tare da samun cikakken iznin masu iko ba.

Haka zalika hukumar da ke yaki da rashin gaskiya a jihar Kano ta na zargin fadar Sarki Sanusi II da saida wasu filaye ba tare da sanin hukumar kula da filayen jihar ba.

Wata majiya a fadar Sarkin ta shaidawa Jaridar Guardian cewa an kirkiro wannan bincike ne domin a cigaba da muzgunawa Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.

A jiya ne The Guardian ta rahoto Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya karyata wadannan zargi da ake jifar gwamnatin Ganduje da su.

A Ranar Lahadi, Muhammad Garba ya bayyana cewa sam babu ruwan Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje a wajen wannan bincike da ake yi a halin yanzu.

KU KARANTA: An fara sulhunta Sarkin Kano Sanusi da Gwamna Ganduje

Kano: Babu rikicin komai tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi II – Inji Kwamishinan labarai
Gwamnatin Ganduje ba ta yin katsaladan a binciken fadar Kano
Asali: UGC

Da ya ke magana, Garba ya nuna cewa hukumar da ke wannan aiki ba ta bukatar a shiga cikin harkarta, domin kuwa duk abin da ta ke yi, ya na da madogara a shari’a.

Kwamishinan jihar ya tunawa jama’a cewa an yi irin wannan bincike a baya, wanda ya taba manyan ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukamai a jihar Kano.

Malam Garba ya ke cewa ko a wancan lokaci, Ganduje bai yi kokarin yi wa hukumar katsalandan ba, ya ma ji labarin binciken ne lokacin da maganar ta shiga gidan jaridu.

Tun ba yau ba, ana dade ana zargin takun-saka tsakanin gwamnatin Abdullahi Ganduje da Sarkin Birni. Wannan har ya kai aka barka masarautar Kano zuwa gidaje biyar.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa babu wata kullaliya tsakanin Abdullahi Ganduje da Sarki, a cewar Kwamishinan, an bi dokokin da su ka dace wajen kara masarautu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel