Jerin Lokutan da Gwamnatocin Tarayya su ka kara farashin mai
1. Yakubu Gowon
Janar Yakubu Gowon shi ne wanda ya fara kara kudin man fetur a lokacin da ya ke mulki. A mulkinsa ne fetur ya tashi daga Kobo 6 zuwa Kobo 8.45 kan kowane lita tsakanin 1966 zuwa 1975.
2. Murtala Mohammed
A cikin watanni shida da Janar Murtala Mohammed ya yi a mulki, ya kara kudin litar man fetur da Kobo 0.55. General Murtala Ramat Muhammed ne ya maida litar man fetur Kobo 9 a Najeriya.
3. Olusegun Obasanjo
Bayan Olusegun Obasanjo ya karbi ragamar mulki a sakamkon kisan Murtala Mohammed, ya kara kudin mai. Gwamnatin Obasanjo ta tada kudin litar mai zuwa Kobo 15.3 a shekarar 1978.
4. Shehu Shagari
A farkon shekarar 1982, shugaban kasa na farko a tsarin shugabancin da ake kai a yanzu, Shehu Shagari ya maida kudin litar mai Kobo 20. Shagari ya yi wannan kari ne sau daya a mulkinsa.
5. Ibrahim Babangida
Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda aka fi sani da IBB ya maida kudin litar mai Kobo 39.5 daga Kobo 20 a 1986. Bayan shekaru biyu kuma Babangida ya maida farashin zuwa Kobo 42.
A Ranar farko a 1989, gwamnatin IBB ta maida mai Kobo 60. Kafin ya sauka ya koma Kobo 70.
KU KARANTA: Haramta Acaba ya sa Jama'a sun fara barin Garin Legas

Asali: Twitter
6. Ernest Shonekan
Duk da Ernest Adegunle Oladeinde Shonekan bai dade a mulki ba, sai da ya kara farashin man fetur daga Kobo 5 zuwa Naira 5. Wannan mummunan karin farashi ya taba mutanen kasar sosai.
7. Sani Abacha
Janar Sani Abacha shi ne ya fara rage farashin mai a lokacin da ya maida kudin lita Naira 3.25 daga Naira 5. A 1994 kuma ya maida litar Man fetur N15, amma daga baya farashin ya koma N11.
8. Abdussalami Abubakar
Janar Abdulsalami Abubakar wanda ya yi mulki daga 1998 zuwa 1999 ya kara farashin litar mai daga Naira 11 zuwa Naira 25. Daga baya ya rage farashin a Junairun 1999 zuwa Naira 20.
9. Olusegun Obasanjo
A shekaru takwas da Olusegun Obasanjo ya yi a kan mulki, ya kara farashin man fetur daga Naira 20 zuwa Naira 75. An yi wannan karin kudin mai a shekarun 2000, 2002, 2003 da kuma 2004.
10. Ummaru Musa Yaradua
Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ya rage kudin litar mai zuwa N65 bayan ya hau kan mulki.
11. Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan ya ba ‘Yan Najeriya goron 2012 da karin man fetur lokacin da ya maida litar mai N141, amma daga baya ya rage farashin zuwa N97. A karshe ya bar mulki mai ya na N87.
12. Muhammadu Buhari
Shugaban kasa mai-ci, Muhammadu Buhari ya kara farashin litar mai daga N87 zuwa N141. An yi wannan karin ne a 2016. Har yanzu ana saida mai ne tsakanin N141 zuwa N145 a kasar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng