An kwantar da tsohon ministan Buhari a asibiti, ya nemi 'yan Najeriya su taya shi da add'ua

An kwantar da tsohon ministan Buhari a asibiti, ya nemi 'yan Najeriya su taya shi da add'ua

An kwantar da tsohon minitsan wasanni da matasa, Barista Solomon Dalung, a wani asibitin birnin tarayya, Abuja, bayan ya kamu da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.

"Ina neman addu'arku, an kwantar da ni a asibiti", kamar yadda tsohon ministan ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (Facebook) ranar Asabar. Amma, bai bayyana irin larurar da yake fama da ita ba.

Sakon na Dalung ya yi farin jini a wurin jama'a, inda suke tofa albarkacin bakinsu tare da bayyana mabanbantan ra'ayoyi.

Wasu manema labarai sun kira lambar tsohon ministan domin neman karin bayani daga gare shi amma bai samu damar amsa kiransu ba.

Dalung, tsohon ministan Buhari daga jihar Filato, bai samu damar koma wa kan kujerarsa ta minista ba duk da yayin yakin neman zaben shugaban kasa ya bugi kirjin cewa babu wani mutum da mace ta haife shi da zai iya hana a mayar da shi kujerarsa.

An kwantar da tsohon ministan Buhari a asibiti, ya nemi 'yan Najeriya su taya shi da add'ua
Solomon Dalung
Asali: UGC

Amma sai gashi babu sunansa a cikin jerin sabbin ministoci da Buhari ya aika wa majalisar dattijai domin ta tantancesu kafin ya nada su a cikin watan Yuli na shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Wani miji ya like al'aurar matarsa da 'super glue' don kar ta ci amanarsa

Ana yawan tuna Dalung, mai shekaru 54, a kan akidunsa na tsauri da tsantseni, lamarin da ya hada shi rigima da hukumar kwallon kwando ta kasa (NBBF) a kan bacewar wasu makudan kudi, $130,000.

Ko a ranar Litinin an ga tsohon ministan a wani filin wasa dake 'Area 3' a unguwar Garki, Abuja, inda ya jagoranci bude wani wasa da aka shirya domin karrama wani tsohon dan jarida mai binciken kwakwaf, Olajide Fashikun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel