Pelosi da wasu ‘Yan Majalisa su na shirin soke sabon tsarin bizar Donald Trump

Pelosi da wasu ‘Yan Majalisa su na shirin soke sabon tsarin bizar Donald Trump

Wasu kusoshi a majalisar tarayyar kasar Amurka ba su goyon bayan gwamnatin Donald Trump na haramtawa ‘Yan Najeriya da wasu kasashe zama a kasar Amurka.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne shugaban kasa Donald Trump ya jefa Najeriya da wasu kasashe biyar cikin jerin wadanda aka haramta masu tarewa cikin Amurka.

Rahotannin da su ka fito daga gidan talabijin na Fox News sun bayyana cewa Nancy Pelosi ta na jan ragama wajen ganin an soke wannan tsari da aka shigo da shi.

Shugabar majalisar wakilai, Pelosi ce ta ke yunkurin ganin an janye wannan tsari na biza da gwamnatin Trump ta kawo, ta na cewa an yi wa kasashen takunkumi.

A Ranar Juma’a, Pelosi ta fito ta na Allah-wadai da matakin da aka dauka na cusa Najeriya da wasu kasashe biyar cikin jerin wadanda ba za su iya zama a Amurka ba.

KU KARANTA: Trump ya yi amai ya lashe a kan rigimar Amurka da Iran

Pelosi da wasu ‘Yan Majalisa su na shirin soke sabon tsarin bizan Donald Trump
Majalisar Wakilai ba ta tare da Trump a kan hana wasu kasashe shiga kasar
Asali: Getty Images

A Ranar 21 ga Watan Junairun 2020, Pelosi ta ce:

“Matakin Gwamnatin Trump na kara fadada mummunar dokar haramtawa mutane shiga Amurka ya ci karo da tsaronmu da kuma dokokin kasa da manufofinmu.”

Shugabar majalisar ta ce: “Wannan doka da ta hana mutane miliyan 350 daga musamman kasashen Afrika damar zama a Amurka, kyamar mutane ne da sunan tsari.”

“Da wannan mataki na rashin tausayi, shugaban kasar ya kara tabbatar da ketarsa tare da wasa da karfin ikon da aka san kasar Amurka a Duniya." Inji Misis Nancy Pelosi.

“Kundin tsarin mulkinmu da tarihinmu ya na alfahari da cewa Amurka kasa ce ta ka zo-na zo.”

Kakakin majalisar ta ce za su yi sauri su kawo kudiri majalisa da zai yi fatali da wannan tsari na Trump da ya sa wa Musulmai takunkumin samun takardun zama a Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel