Manyan PDP su na kokarin tsige Shugaban jam’iyya, Secondus kafin 2021

Manyan PDP su na kokarin tsige Shugaban jam’iyya, Secondus kafin 2021

Jagororin jam’iyyar hamayya ta PDP a Kudu maso Yammacin Najeriya sun fara tattauna da yakin ganin an sauke Uche Secondus daga kan kujerar shugaban jam’iyya.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Lahadi, wadannan jiga-jigai na jam’iyyar adawa, sun fara karkato da hankalin ‘Yanuwansa domin cin wannan manufa ta su.

Prince Uche Secondus wanda sai shekarar 2021 wa’adinsa na shekaru hudu a ofis zai kare, ya shiga cikin tsaka mai wuya ne a dalilin rikicin da PDP ta samu kanta a ciki.

Rigingimun da ake yi a jihohi da yawan sauya-sheka, sabanin majalisar wakilai, da kuma keta dokokin jam’iyya ya na cikin matsalolin da Uche Secondus ya samu.

Haka zalika manyan jam’iyyar su na ganin laifin majalisarsa ta NWC wajen gaza kai jam’iyyar ga ci a zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar da ta wuce watau 2019.

KU KARANTA: Jigon APC ya yi kaca-kaca da Gwamna Ganduje da Shugaban Jam'iyya

Manyan PDP su na kokarin tsige Shugaban jam’iyya, Secondus kafin 2021
Ana neman tsige Shugaban jam’iyyar PDP Uce Secondus daga mukaminsa
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a Ranar 2 ga Watan Fubrairu cewa ana yunkurin sauke Uche Secondus daga kujerarsa kafin wa’adinsa ya kai ga cika a shekarar badi.

Majiyar Jaridar ta ce wasu wadanda aka kafa jam’iyyar da su, da tsofaffin gwamnoni, da ‘Yan majalisu su na cikin masu kokarin ganin bayan Uche Secondus a PDP.

Rahotanni sun ce fusatattun ‘Ya ‘yan jam’iyyar su na kokarin zuga tsohon gwamnan Ogun, Olagunsoye Oyinlola, ya dawo ya nemi kujerar Shugaban jam’iyya na kasa.

Ana tunanin cewa yin hakan zai sa ‘Yan adawar Yankin Kudu maso Yammacin kasar su ji cewa ana damawa da su a cikin tafiyar PDP ganin yanzu ba su da wuri sosai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel