Babu ruwan Dangi da shari’ar da za ayi da Obasanjo a kotu Ogun - Sogunro

Babu ruwan Dangi da shari’ar da za ayi da Obasanjo a kotu Ogun - Sogunro

Mutanen Dangin Sogunro da ke cikin garin Itele-Ota a karamar hukumar Ado/Odo Ota a jihar Ogun sun ce ba su da hannu wajen kai karar Janar Olusegun Obasanjo kotu.

A makon nan Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutanen na Sogunro sun musanya hannu a karar da aka kai tsohon shugaban kasar a kotu saboda rikici a kan wani fili.

Wadanda su ke da hannu a wannan karar sun hada da Cif Nurudeen Akanbi Akapo, Sunday Mathew Owotolu, Taoreed Momodu Dada da wani Monsuru Ashifatu Yusuf.

Wadannan Bayin Allah sun kai Obasanjo, da kaninsa Abraham Idowu Akanle da kuma Mai dakinsa kara ne a babban kotun da ke Garin Ota a game da cinikin wani fili.

Masu karar su na kuka ne da takardun bogi da aka ba su na wani fili a Itele da ke cikin Garin Sogunro kamar yadda wani ‘Danuwansa, Sunday Sogunro, ya bayyana jiya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun hallaka Matar wani Likita da aka sace a Kaduna

Babu ruwan Dangi da shari’ar da za ayi da Obasanjo a kotu Ogun - Sogunro
'Yanuwan Obasanjo sun ce ba su su ka kai shi kotu ba
Asali: Twitter

Honarabul Sunday Sogunro ya yi wannan bayani ne a cikin karshen makon nan a Garin Ota ya na mai cewa babu hannunsu a karar da aka kai Obasanjo da 'Danuwansa.

Sogunro da ya ke magana tare da wasu ‘Yanuwan tsohon Shugaban kasar da mutanen Kauyensa, ya bayyana cewa ba su su ka kai tsohon Sojan kara a gaban Alkali ba.

Hon. Sogunro ya bayyana cewa wadanda su ka shigar da karar, sun yi haka ne don ganin damarsu. Wannan Bawan Allah shi ne mai magana da yawun dangin.

A wajen wannan zantawa da aka yi da Manema labarai, an hangi ‘Yanuwa da Abokan arzikin Dangin tsohon shugaban kasar dauke da wasu takardu masu isar da sako.

Dangin tsohon shugaban kasar sun bayyana cewa wannan kara bai tada masu hankali ba domin babu wata doka da aka saba wajen cinikin filin da ake faman rikici a kansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel