Wata sabuwa: EFCC ta haramtawa masu aure neman aikinta

Wata sabuwa: EFCC ta haramtawa masu aure neman aikinta

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta haramtawa masu aure neman aikint wanda ta bude kwanan nan

- NECA kuwa ta kalubalanci hukumar tare da bayyana cewa hakan ya ci karo da dokar kungiyar kwadago ta duniya

- Babban daraktan NECA, Timothy Olawale ya ce ba a bayyana dokokin daukar aiki karara kamar yadda hukumar tayi

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta haramtawa mutane masu aure shiga sahun masu neman aikin hukumar.

Hukumar ta bada wannan sanarwar ne a cikin ka'idojin da mai neman aiki a hukumar zai cike kafin a dube shi.

Wannan hukuncin kuwa ya jawo musu cece-kuce daga Nigeria Employers Consultative Association, NECA, kungiyar da ke da dangantaka da kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC.

Babban daraktan NECA, Timothy Olawale, ya sanar da jaridar The Punch cewa wannan dokar ta EFCC ta sha banban da dokokin kungiyar kwadago ta duniya.

Wata sabuwa: EFCC ta haramtawa masu aure neman aikinta
Wata sabuwa: EFCC ta haramtawa masu aure neman aikinta
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

Kamar yadda ya ce, matsalar wariya ita ce babbar matsalar da muke fuskanta a kasar nan.

A cewarsa: "Muna neman hanyar tafiya tare da kowa ne. Wannan ne dokar daidaituwa da adalci wajen daukar aiki. Abinda EFCC din tayi ya ci karo da dokokin ILO."

"A yayin diban ma'aikata, ba a ware wasu mutane. Idan za a saka wasu dokoki a yayin daukar aiki, ba a bayyanawa jama'a. A kan bar shi ne a matsayin sirri. Wanne laifi masu aure suka yi?" Cewar babban darakta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel