Abin da ya faru yayin da Sowore ya ziyarci wata Makaranta domin ya koyar

Abin da ya faru yayin da Sowore ya ziyarci wata Makaranta domin ya koyar

An gamu da ‘yar takaddama a Ranar Litinin, 27 ga Watan Junairu a wata makaranta a Garin Abuja saboda ziyarar Omoyele Sowore.

‘Dan gwagwarmayan wanda yanzu ya shiga harkar siyasa gadan-gadan ya bukaci ya koyar da Daliban wata Makarantar gwamnati.

Mista Sowore ya bayyana cewa ya nemi Makarantar da zai koyar da darasin ilmin gwamnati da ilmin kasa da zama haka kawai a Gari.

Omoyele Sowore ya shirya da shugaban wata Makaranta da cewa zai koyar da Dalibansa. Ko da ya zo makarantar sai kuma labari ya canza.

A cewar Sowore, da ya iso Makarantar sai ya iske shugaban makarantar ya tsere ya bar shi da yara. Wannan ya sa ransa ya yi dubu ya baci.

KU KARANTA: An tsinci gawar wani Almajiri a Garin Kano

“Watakila wannan ya ba ku dariya ko ku kagara jin yadda aka yi, yau na shirya na nemi makarantar gwamnati da zan koyar a Abuja...”

“...In koyar da ilmin aikin gwamnati ko ilmin kasa yayin da na ke zama dinkim-dinkim a Abuja, sai na shirya da wata makarantar gwamnati.”

“Amma lokacin da mu ka isa, sai mu ka ga shugaban makarantar ya tsere.” Inji Sowore.

Babu mamaki shugaban makarantar ya ji tsoron jefa kansa cikin matsala ne ganin cewa ana zargin Yele Sowore a kotu da manyan laifuffuka.

Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu kan lamarin, wasu su na yabawa kwazon Sowore, yayin da wasu ke ganin hangen-nesan shugaban makarantar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel