Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: An tsinci gawar wani almajiri a Kano

Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un: An tsinci gawar wani almajiri a Kano

- Al’ummar unguwar Dorayi karama sun kama wani mutum mai suna Musa da ya jefar da gawar wani almajiri

- Al’amarin ya faru ne yammacin jiya Laraba amma sai wata mata mai suna Amina ta hango shi ta Katanga

- Matasan unguwar ne basu aminta da abinda mutumin ya aje ba, hakan yasa suka yi tara-tara suka damke shi tare da mika wa ‘yan sanda

Al’ummar Unguwar Dorayi karama sun kama wani mutum mai suna Musa da ya jefar da gawar wani almajiri mai suna Nasir a yankin.

Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Laraba, in da wata mata mai suna Amina ta hango shi ta Katanga a yayin da ya jefar da gawar. Ya yi wa matar barazanar cewa zai halakata, kamar yadda ta shaidawa gidan rediyon Dala.

Innalillahi: An tsinci gawar wani almajiri a Kano
Innalillahi: An tsinci gawar wani almajiri a Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jama'ar Zaria sun maka rundunar sojin Najeriya a kotu

Wasu shaidun ganau ba jiyau ba sun tabbatar wa da gidan rediyon Dala FM cewa sun ga gawar almajirin an rufe ta a cikin wani abu, da alama kuma har ta fara sauya kamanni. Ganin basu aminta da abinda aka ajiye din bane yasa suka yi tara-tara suka damke mutumin da ya ajeta.

Rahotanni daga unguwar na cewa wanda aka kashe din wani almajiri ne mai suna Nasiru wanda aka dau tsawon kwanaki biyar kenan malamin sa na neman sa.

Hakazalika, al’ummar unguwar sun shaidawa Dala FM cewa ‘yan sanda sun cafke matashin da ya jefar da gawar tare da uwar dakin almajirin.

Sai dai har yanzu bamu samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ba, sai dai zuwa nan gaba idan an samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel