KAROTA: Mun samu kudin shiga na N362.9m a Kano – Inji Dan Agundi

KAROTA: Mun samu kudin shiga na N362.9m a Kano – Inji Dan Agundi

Baffa Dan-Agundi, wanda shi ne babban Darektan hukumar KAROTA mai kula da hanya a jihar Kano, ya bayyana shirin da su ke yi a fadin jihar.

Hon. Baffa Dan-Agundi, ya bayyana cewa kawo yanzu KAROTA ta yi wa masu Keke Napep fiye da 58, 986 rajista a wani tsari da su ka shigo da shi.

KAROTA ta kawo wata na'urar zamani domin ta takaita faruwar laifuffuka a jihar. Dan-Agundi ya bayyana wannan da ya zanta da Manema labarai.

Shugaban hukumar KAROTA ya bayyana cewa sun samu Naira miliyan 362.9 daga wajen wadannan Matuka fiye da 58, 000 da su ka yi wa rajista.

“Wannan na'ura da mu ka kawo ta fara aiki yanzu, domin mun gano wani Direba da ya tsere da kayan wani Bawan Allah a cikin Keke Napep dinsa.”

KAROTA: Mun samu kudin shiga na N362.9m a Kano – Inji Dan Agundi
KAROTA MD ya ce kudin da aka samu da A-Daidata-Sahu su na nan
Asali: Twitter

“Mun samo Direban da ya tsere da kayan fasinja, mun san shi kuma za mu kama shi, mu mika shi hannun ‘Yan Sanda. Za mu hana sa sana’ar Daidaita sahu.”

Shugaban hukumar ya bayyana cewa: “An kafa na’urar bibiyan Direba ne da salula da kuma layin wayarsa domin a iya gano inda masu laifi su ka shige.”

A cewar Babba Dan-Agundi, rade-radin da wasu ke yi na cewa makudan miliyoyin kudin da aka tara daga rajistar Keke-Napep sun bace, ba gaskiya bane.

Hukumar ta ce kudin da ta samu su na cikin wani asusun banki da ke Baitul-Malin gwamnati. A na su bangaren, Direbobi sun ce za su bada goyon bayansu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel