Majalisa: Ahmad Lawan ya rantsar da Sanata Christopher Ekpeyong

Majalisa: Ahmad Lawan ya rantsar da Sanata Christopher Ekpeyong

Sabon Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, Christopher Ekpeyong, ya tabbata ‘Dan majalisar dattawa bayan an sake rantsar da shi.

A yau Alhamis, 30 ga Watan Junairun 2020, aka rantsar da Sanata Christopher Ekpeyong a matsayin Mai wakiltar Akwa Ibom a Majalisa.

Mai girma Sanata Ahmad Ibrahim Lawan da kansa ne ya rantsar da Sanatan a zauren majalisa. Hakan na zuwa ne bayan ya lashe zaben da aka yi.

Christopher Ekpeyong shi ne ya karbe kujerar Sanata Godswill Akpabio wanda ya rike gwamnan jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Sanata Ekpeyong ya lashe zabe ne a karkashin jam’iyyar PDP. Daga baya kotu ta rusa nasararsa, ta kuma bukaci a sake gudanar da zabe a wasu wurare.

KU KARANTA: Kungiya ta goyi bayan Sanatan da ya nemi Buhari ya yi murabus

Majalisa: Ahmad Lawan ya rantsar da Sanata Christopher Ekpeyong
Christopher Ekpeyong ya dare kujerar Akpabio daram-dam-dam
Asali: Depositphotos

Bayan an gudanar da zabe a Ranar 25 ga Watan Junairun nan kamar yadda kotun daukaka kara ta bukata, jam’iyyar PDP ce dai ta sake samun nasara.

Ekpeyong ya zama Sanata ne da karfe 10:40 na safiyar Alhamis bayan mataimakin Akawun majalisar, Musa Abdullahi, ya karanto masa rantsuwa.

Sanatan ya dawo kan kujerarsa ne bayan Sanatocin sun tattauna game da zaman da aka yi jiya Laraba. Wannan shi ne tsarin da aka saba yi a majalisar.

Sanata Akpabio shi ya wakilci Arewa maso gabashin Akwa Ibom a majalisar baya da ta shude. Ya kuma rike shugaban marasa rinjaye kafin ya koma APC.

Idan ba za ku manta ba, Godwill Akpabio wanda yanzu ya zama Minista, ya bukaci a maye gurbinsa da wani ‘Dan takarar, amma INEC ta ki yarda.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel