Hajji: Zan zabtare kudin mahajatta – Zababben Shugaban NAHCON ya yi alkawari

Hajji: Zan zabtare kudin mahajatta – Zababben Shugaban NAHCON ya yi alkawari

- Kwanan nan Musulmai za su samu garabasar zuwa aikin Hajji a kasar Saudiyya yayinda Zhikrullahi Hassan, zababben Shugaban hukumar aikin hajji ya yi alkawarin yanke farashin kudin da ake biya

- Hassan ya fadi hakan ne a lokacin da majalisar dattawa ke tantance shi, inda ya bayyana cewa yunkurin zai ba al’umman Najeriya damar zuwa sauke farali

- Zababben Shugaban ya kuma bayyana cewa zai kafa wani shiri na tanadin Hajji ga maniyyata idan aka tabbatar da nadinsa

Kamar yadda kuka sani zuwa aikin Hajji na daya daga ciki manyan shika-shikan addinin Musulunci. Hakan ne ya duk Musulmi a fadin duniya ke daukar aikin hajjin da muhimmanci sosai.

Abun bakin ciki, sai gashi tattalin arziki, musamman a kasashen da ke tasowa irin Najeriya, ya sanya Musulmai da dama rashin samun damar zuwa kasa mai tsarki don sauke farali sakamakon yawan kudin a ake karawa duk shekara.

Hajji: Zan zabtare kudin mahajatta – Zababben Shugaban NAHCON ya yi alkawari
Hajji: Zan zabtare kudin mahajatta – Zababben Shugaban NAHCON ya yi alkawari
Asali: UGC

Don haka, ga dukkan alamu lokacin da yan Najeriya da yawa za su samu zuwa aikin hajji ya kusa yayinda Zhikrullahi Hassan, zababben Shugaban hukumar aikin hajji na kasa, ya yi alkawarin yanke kudin Hajjin idan majalisar dattawa ta tabbatar da nadin nasa.

Da yake jawabi ga majalisar dattawa a lokacin tantancewarsa, Hassan ya ce kudin hajji yanzu ba abune da mutane ke iya biya ba kuma akwai bukatar sake duba lamarin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa irin wannan yunkurin ba zai bari al’umman Najeriya da ke burin sauke farali samun damar yin hakan ba.

Hassan ya kuma ce zai kafa shirin tara kudin hajji wanda zai ba maniyyata damar tara kudi a hankali kafin lokacin hajjin.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta bukaci Buhari da ya sanya dokar ta baci kan tsaron kasar

Ya kuma bayyana cewa zai tabbatar da ganin an rage yawan kwanakin da yan Najeriya ke shafewa a kasar Sauddiyya a lokacin aikin hajji, inda ya ce yan Najeriya na dadewa da yawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel